Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ranar yaki da miyagun kwayoyi: Ana gudanar da ayyuka daban daban na yaki da miyagun kwayoyi a fadin kasar Sin
2020-06-26 12:05:57        cri

Ranar 26 ga watan Yuni rana ce ta yaki da miyagun kwayoyi ta kasa da kasa karo na 33. Daga watan Janairu zuwa Mayun shekarar 2020, hukumomin shigi da fici na kasar Sin sun gano matsalolin dake shafar ta'ammali da kwayoyi kimanin 829 inda suka kwace kilogram na kwayoyi 4,792. An gudanar da aikin binciken haramtattun kwayoyi masu yawa a duk fadin kasar Sin da aikin wayar da kan al'umma game da illolin ta'ammali da miyagun kwayoyi, da kuma kaucewa amfani da kwayoyi masu hadari.

Bisa sanarwar da hukumar shigi da fici ta kasar Sin ta fitar, daga watan Janairu zuwa Mayun shekarar 2020, hukumomin kula da aikin shigi da fici sun yi nasarar gano batutuwan ta'ammali da miyagun kwayoyi kimanin 829 kana sun kwace haramtattun kwayoyi masu nauyin kilogram 4,792, wanda ya kunshi hodar koken kilogram 671, kwayar maganin methamphetamine kilogram 3494, da kilogram 572 na sinadarin opium, da wasu kwayoyin magungunan kilogram 55. Hukumar dake yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi dake kan iyokin kasar tana fama da gagarumin aiki. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China