Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daliban Afrika dake kasar Sin: Mun gode da dukkanin wani taimako da Sinawa suka ba mu
2020-06-24 14:29:00        cri


A shekarun baya-baya nan, matasan Afrika masu tarin yawa sun zo nan kasar Sin don kara iliminsu, sun kuma zama wata gada ta sada zumunta tsakanin Sin da Afrika. Ban da wannan kuma, wadannan matasa suna hadin kai da abokansu Sinawa wajen yakar COVID-19, suna kokarin ba da taimakon sa kai bisa jagorancin makarantu, kuma sun nuna godiya matuka ga malamai da dalibai Sinawa dake ba su taimako.

Tiando S. Damien, matashi ne dan kasar Benin, wanda ya yi karatun digiri na 3 a jami'ar koyon ilmin yanayin kasa ta kasar Sin dake birnin Wuhan. Bayan barkewar cutar COVID-19, ya jagoranci wata kungiyar sa kai dake cikin jami'ar mai mambobi daga kasashe 13 mai sunan "Iron Man", wadda ta ba da taimako ga makarantar, kan ayyukan jigilar kayayyaki, da rarraba abinci da dai sauransu, matakin da ya ba da tabbaci ga zaman rayuwar daliban kasashen ketare 320.

Yayin da ake tsaka da yakar cutar, aikin sa kai na bukatar jarumtaka, kamar yadda "Iron Man" ya yi, ana kuma bukatar gudanar da aikin cikin natsuwa.

Damien ya yi bayanin cewa, lokacin da yake samarwa dalibai kayayyakin da suke bukata, zai buga kofofinsu har sau uku, daga baya kuma bayan mintoci 20 dalibai za su fito su dauki wadannan kayayyaki domin rage cudanya.

"Bai kamata mu kusanci juna ba, balle mika kayayyaki hannu da hannu, hakan na tabbatar da tsaronmu."

Wani mai sa kai a cikin wannan kungiya, dan Najeriya Oscar Chijioke Nkwazema ya ce, ko da yake yana shan aiki a ko wace rana, amma yana farin ciki sosai domin ba da taimako ga saura. Ya ce:  

"Shiga wannan kungiya yana da ma'ana sosai a rayuwata, muna taimakawa juna ta hanyar sa kai, don tinkarar mawuyancin hali. Ina alfahari matuka saboda baiwa sauran dalibai taimako."

Ana farfado da karatu a makarantu sannu a hankali bisa aikin kandagarki da ake gudanarwa. A jami'ar Dongnan dake birnin Nanjing, yawan daliban ketare ya wuce 1100, 600 suna nan kasar Sin yayin barkewar cutar, daga cikinsu kashi 40% dalibai ne daga Afrika. Kwanakin baya, wasu daliban ketare na kwalejin koyar da daliban ketare sun koyi dafa Jiaozi daga malaman su Sinawa. Wani dalibi daga Tanzaniya mai suna Kassim Issa Suwedi ya ce:  

"Dalibai suna cikin makaranta a wadannan lokuta, saboda haka makaranta ta gudanar da wasu ayyuka don faranta mana rai."

An ce, jami'ar Dongnan ta hana shige da fice tun barkewar cutar. An kafa kasuwar sayar da kayayyakin yau da kullum a cikin jami'ar, don tabbatar da biyan bukatun dalibai. Ban da wannan kuma, jami'ar ta kafa kungiyar sa kai ta dalibai, don taimakawa aikin tattara bayanan mutanen da suka bar yankin dakunan kwana da dai sauransu, da ayyuka masu alaka. Malama Yin Guo na kwalejin koyar da daliban ketare ta ce:  

"Wasu daliban ketare su ne jakadan dalibai, suna tuntubar sauran dalibai don isar da wasu muhimman bayanai tsakanin dalibai da makaranta. Idan akwai bukata, za mu iya kai wadannan bayanai zuwa ga rukunin yakar cutar na jami'armu."

A halin yanzu, ana shiga lokacin kama karatu, a cewar malama Yin Guo, jami'ar tana samar wa daliban ketare wasu bayanai game da neman guraben aikin yi, ta ce:

"Dalibai suna iya yin rajista a kan manhaja, sannan mun tuntubi wasu kamfanoni. Daga bisani kuma, za a gabatar da jadawali, da wuri da kuma lokacin da za a gudanar da taron neman aikin yi a kan manhajar Wechat. "

Oscar Chijioke Nkwazema, dan Najeriya wanda ke karatun ilimin injiniya a jami'ar koyon ilmin yanayin kasa ta kasar Sin, yayin da ya waiwayi wannan cuta dake bulla cikin gaggawa ya ce:  

"Ina godiya ga wadanda suke ba mu taimako, kuma na gode sosai kan matakan da jami'armu ta dauka." (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China