Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin Watsa Labaru Na Afirka Sun Darajta Tasirin Taron Kolin Musamman Na Sin Da Afirka Game Da Hadin Kan Yakar COVID-19
2020-06-23 14:21:50        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya shugabanci taron koli na musamman game da hadin kan yakar cutar COVID-19 a tsakanin Sin da Afirka, taron da aka shirya ta kafar bidiyo a ranar 17 ga wata a nan birnin Beijing. A yayin jawabi da ya yi a gun taron, ya jaddada cewa, ya kamata a tsaya kan hadin kai wajen dakile annobar, da inganta hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka, da bin ra'ayin bangarori da dama, da kuma kara sada zumunta a tsakanin bangarorin biyu.

A 'yan kwanakin da suka gabata, wasu muhimman kafofin watsa labaru na Afirka, sun jinjinawa shawarwarin da shugaba Xi ya gabatar, tare kuma da yayata labaru, da bayar da sharhi kan wannan batu.

Manyan jaridu guda biyu na kasar Sudan ta kudu, da jaridar Juba Monitor, da jaridar The Dawn, sun yayata da cikakken jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a gun taron koli a muhimman shafukan su.

 

 

Baya ga haka, wadannan kafofin watsa labaru, sun nuna yabo sosai ga kasar Sin, kan kokarin da take yi na hada kai da kasashen Afirka, wajen kiyaye tsarin gudanar da harkokin duniya dake karkashin jagorancin MDD, da nuna goyon baya ga kungiyar WHO, don kara taka muhimmiyar rawa a ayyukan yakar annobar na duniya. A ganinsu, wannan na da ma'ana kwarai a fannin tattara ra'ayin bai daya na kasashen duniya, game da yaki da annobar, da kawar da tasirin da aka samu a fannin siyasa.

Gidan talibijin na ETV na kasar Afirka ta kudu ya watsa bidiyo game da yadda shugaba Xi Jinping ya yi jawabi a gun taron. Ban da wannan kuma, shafin yanar gizo na gwamnati, da na Independent Media da jaridar The Citizen, da ma sauran kafofin watsa labarum kasar ta Afirka ta kudun, su ma sun bayar da labarai kan jawabin da shugaba Xi Jinping ya yi, inda suka ruwaito abubuwan dake cikin jawabin, da suka shafi gudanar da hadin kai a tsakanin Sin da MDD, da WHO, da ma sauran abokanta, wajen taimakawa kasashen Afirka a fannin yakar annobar.

 

 

Sun tabbatar da cewa, kasar Sin na goyon bayan kasashen Afirka wajen raya yankin cinikayya cikin 'yanci a nahiyar Afirka, kuma Sin za ta ci gaba da hadin kai tare da kasashen Afirka, a fannonin tattalin arziki na fasahar zamani, da gudanar da harkokin birane ta hanyar zamani, da tsimin makamashi, da fasahar 5G da dai makamatansu. Kana Sin za kuma ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan kara sada zumunci a tsakaninta da Afirka da dai sauransu.

Baya ga haka, kamfanin dillancin labaru na kasar Somaliya, da jaridar "The Dawn" ta Najeriya, da jaridar Le Soleil ta kasar Senegal da dai sauransu, su ma sun nuna yabo sosai kan shawarwarin da shugaba Xi Jinping ya gabatar, a yayin taron koli game da hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka. A cikin shahin da wadannan muhimman kafofin watsa labaru suka bayar, ana ganin cewa, shawarwarin sun nuna tunanin hadin kai da taimakawa juna a tsakanin Sin da Afirka, kana ya kara nuna tsayayyan goyon baya da Sin ke bayarwa, a fannin ci gaban tattalin arziki da zaman al'ummar kasashen Afirka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China