![]() |
|
2020-06-23 10:00:48 cri |
Jakadan kasar Sin ya mika kashi na biyu na tallafin kayayyakin kiwon lafiya ga kasar Saliyo a ranar Litinin, domin taimakawa kasar a yakin da take da annobar COVID-19.
Tallafin kayayyakin sun hada da kayan gwaje-gwaje 10,032, da kayan bada kariya ga jami'an lafiya 5,000, da kayan taimakawa numfashin samfurin N95 guda 5,000, da takunkumin rufe fuska 150,000, gilashin rufe fuska na likitoci 7,000, da safar hannun likitoci 7,000, sai takalman likitoci 3,000.
Ministar harkokin wajen kasar Saliyo Nabeela Tunis, ta ce gudunmawar wata shaida ce dake bayyana irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Shi ma ministan lafiyar kasar Saliyo Alpha Tejan Wurie, ya godewa kasar Sin bisa ga taimakon da ta baiwa kasarsa. Ya kara da cewa, ana iya gane amini na kwarai ne yayi da ake cikin halin bukata. (Ahmad)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China