Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kara tsaurara matakan kandagarkin COVID-19 a Beijing
2020-06-19 13:56:21        cri
A kwanakin baya bayan nan, hukumomi a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, sun ba da rahoton samun sabbin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, inda nan take ba tare da bata lokaci ba, mahukuntan birnin suka dauki managartan matakai na hana yaduwarta, aka fara gudanar da cikakken bincike kan yanayin yaduwar cutar a kewayen kasuwar da aka gano kwayar cutar, wato kasuwar Xinfadi, inda mutane da dama ke taruwa, kuma ke cinikin amfanin gona da na ruwa a ko wace rana.

A sa'i daya kuma an fara yin gwajin kwayar cutar ta makogwaro a dukkan muhimman sassan birnin, da kara fadada yin gwaje-gwaje, don gano wadanda suka kamu da cutar, da ma wadanda ba su nuna alamun kamuwa da ita ba.

Dalilin da ya sa aka dauki matakan kandagarkin a kan lokaci shi ne, manufar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa, wato mayar da moriyar al'ummun kasar a gaban komai. Hakika shugaban kasar Xi Jinping ya taba jaddada muhimmancin manufar sau da dama a wuraren daban daban, inda ya bayyana cewa, tsaron al'ummun kasa abu ne mafi muhimmanci ga tsaron kasa, don haka dole ne a kafa tsarin kiyaye kiwon lafiyar jama'a, kuma a kyautata tsarin yin gargadi kan aukuwar abubuwa na ba zata, haka kuma a daga matsayin kandagarkin cuta, ta yadda za a tabbatar da tsaron lafiyar al'ummun kasar.

Kana tun daga yammacin ranar 16 ga wata, birnin Beijing ya maido da matakan yaki da cutar COVID-19 zuwa matsayi na biyu, ana kuma ci gaba da gwada zafin jikin mazauna unguwanni, tare kuma da yin rijistar masu shiga da fita daga unguwannin. Ban da haka kuma, daliban makaranta suna ci gaba da karatu a gida ta yanar gizo.

Kokarin da daukacin mazauna birnin Beijing suke a karkashin jagorancin mahukuntan birnin ya nuna cewa, mazauna birnin sun amince da matakan da mahukuntan birnin suke dauka, saboda sun fahimci cewa, makasudin daukar matakan hana yaduwar cutar shi ne, tabbatar da tsaron rayukansu, wanda hakan ya nuna cewa, mazauna birnin suna cike da imani kan sakamakon da za a samu, don haka ana sa ran cewa, birnin Beijing zai yi nasarar ganin bayan cutar ba tare da bata lokaci ba.

Hakan dai ya yi daidai da tsokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi, a yayin taron kolin Sin da Afirka na musamman, kan hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19 da aka kira ta kafar bidiyo a Laraba ranar 17 ga wata, inda ya furta fatan bil Adama, na dakile annobar, da ci gaba da zaman rayuwa cikin nishadi. (Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China