Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a kaddamar da gangamin yaki da fyade a Nijeriya
2020-06-19 11:15:12        cri
Ministan yada labarai da al'adu na Nijeriya Lai Mohammed, ya bayyana a jiya cewa, kasar ta shirya kaddamar da gangamin yaki da fyade da cin zarafin wani jinsi a kasar.

Da yake jawabi yayin wani taro a Abuja, babban birnin kasar, Ministan ya ce gwamnati za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen dakile mummunan ta'adar daga ci gaba da kamarin da ya kai ga samun rahoton fyade 717 tsakanin watan Junairu zuwa Mayu.

Babban Sufeton 'yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya shaidawa manema labarai a ranar Litinin cewa, kimanin mutanen da ake zargi da laifin fyade 799 rundunarsa ta kama, wadanda aka ce suka aikata laifukan fyade 717, daga watan Junairu zuwa Mayun bana.

Mohammed Adamu, ya kara da cewa, gangamin ya zama dole, ba kawai don kara wayar da kai game da matsalar ba, har ma da tabbatar da 'yan Nijeriya sun yake ta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China