Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masaniļ¼šAn yi nasarar shawo kan COVID-19 da ta bulla a Beijing
2020-06-18 20:22:04        cri
Babban masanin Ilimin yaduwar cututtuka a cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin Wu Zunyou, ya bayyana cewa, an yi nasarar shawo kan cutar COVID-19 da ta bulla a birnin Beijing, kuma ana saran yawan sabbin masu kamu da cutar zai ragu nan da 'yan kwanaki.

Wu wanda ya bayyana haka yayin taron manema labarai Alhamis din nan, ya ce, ko da yake mahukuntan birnin na sanar da duniya rahoton wadanda suka kamu da cutar a kowace rana, hakan ba ya nufin cewa, dukkan wadanda suka kamu da cutar sabbi ne. Yana mai cewa, mutane 21 da aka ba da rahoton sun kamu da cutar a Beijing a ranar Laraba, sun kamu da cutar ce kafin ranar 12 ga watan Yuni.

Sai dai ya ce, ana saran samun karin masu kamuwa da cutar cikin kwanaki masu zuwa, amma adadin zai ragu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China