Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Niger: kasar Sin ta ba da gudummowa wajen yaki da annobar COVID-19 a duniya
2020-06-18 10:46:03        cri

Jiya Laraba 17 ga wata, fadar shugaban janhuriyar Nijar, ta bayyana a shafin sada zumunta cewa, shugaban kasar Mouhamadou Issoufou, kuma shugaban kungiyar kawancen kasashen yammacin Afirka wato ECOWAS, ya halarci taron koli na musamman ta kafar bidiyo tsakanin kasashen Sin da Afirka, kan yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19.

A cikin jawabinsa yayin taron, Mouhamadou Issoufou ya ce, kasashe mambobin ECOWAS sun jinjina, da kuma goyon bayan huldar abota a tsakanin kasashen Sin da Afirka, bisa tsarin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka.

Ya ce irin wannan kyakkyawar hulda, ta kara azama kan hadin kan bangarorin 2 wajen yaki da annobar. Yana ganin cewa, gwamantin Sin ta nuna gwaninta wajen dakile da kandagarkin annobar, lamarin da ya sanya kasashen Afirka ke kara girmamawa da kuma yaba mata.

Shugaban ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ta ba da gudummowa ta hanyar yin hadin kai da kungiyar tarayyar Afirka wato AU, da MDD, da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, wajen yaki da annobar a duniya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China