Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yaki da COVID-19 cikin hadin gwiwa
2020-06-18 00:46:30        cri

Yaki da COVID-19 cikin hadin gwiwa

Jawabin Shugaban Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin Xi Jinping, yayin taron kolin musamman na Sin da kasashen Afirka kan yaki da COVID-19 cikin hadin gwiwa

 

 

Mai Girma Shugaba Cyril Ramaphosa,

Mai Girma Shugaba Macky Sall,

Masu girma shugabannin kasashe da gwamnatoci,

Mai girma shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat,

Mai girma, babban sakataren MDD, Antonio Guterres,

Mai girma, babban darektan hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus

A wannan lokaci mai muhimmanci da duniya ke yaki da COVID-19, mun halarci wannan taron kolin na musamman na Sin da Afirka. Tsoffin abokai da sabbi, sun hallara ta kafar bidiyo don tattauna matakan da muke dauka kan yaki da annobar COVID-19 tare da sabunta alaka tsakanin Sin da Afirka. Ina godiya ga shugaba Ramaphosa da shugaba Sall, kan yadda suka ba da hadin kai wajen shirya wannan taron koli, ina kuma yabawa dukkan abokan da suke tare damu a wannan lokaci. Ina kuma son na mika godiyata ga sauran shugabannin Afirka da ba su samu damar kasancewa tare da mu a yau ba.

Annobar COVID-19 da ta bulla ba zato ba tsammani, ta yi illa a wasu kasashen duniya, inda ta hallaka dubban daruruwan rayuka. A nan, ina ganin, ya kamata mu yi shiru na minti guda don girmamawa wadanda suka kwanta dama sanadiyar COVID-19 tare da mika ta'aziya ga iyalansu.

Yayin da ake fama da COVID-19, Sin da Afirka sun jure manyan kalubale. Al'ummar Sinawa sun hada kai tare da sadaukar da kai wajen yakar wannan annoba a kasar. Har yanzu, muna taka-tsantsan kan hadarin sake yiwuwar bullar cutar. A nasu bangare, gwamnatoci da jama'a a Afirka, sun hada kai, karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afirka, sun dauki managartan matakai, wajen rage yaduwar cutar. Wadannan matakai sun haifar da kyakkyawan sakamako.

A bangaren yaki da COVID-19, Sin da Afirka sun taimakawa juna da kasancewa kafada da kadafa da juna wajen yaki da wannan annoba. Har kullum kasar Sin ba zata manta da goyon bayan da Afirka ta ba mu ba, lokacin da muke yaki da wannan annoba. Domin yaba kyauta, lokacin da cutar ta bulla a Afirka, kasar Sin ce ta farko da ta garzaya don taimakawa nahiyar, kuma har yanzu tana nan daram tare da al'ummar Afirka.

A fannin yaki da wannan annoba, Sin da Afirka sun karfafa alaka da goyon bayan da amincewa da juna. Ina son in jaddada kudirin kasar Sin kan dadadden alakar dake tsakaninta da Afirka. Duk wata bahaguwar fahimta da wasu kasashen duniya za su yiwa alakarmu, kasar Sin ba za ta taba yin kasa a gwiwa wajen karfafa alaka da nuna goyon baya ga Afirka ba.

Abokai

Har yanzu cutar COVID-19 tana yin barna a wasu sassan duniya. Sin da Afirka suna da nauyi a wuyansu wajen yakar wannan annoba, yayin da suke kokarin daidaita tattalin arziki da kare rayukan al'ummominsu. Wabiji ne mu ba da muhimmanci ga batun da ya shafi jama'armu da kuma rayukansu. Wajibi ne mu samar da albarkatu, da nacewa kan alakarmu, sannan mu yi duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da lafiyar jama'a da ma takaita yaduwar COVID-19.

Da farko, wajibi ne mu himmatu wajen yaki da COVID-19 tare. Kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa matakan Afirka na yaki da wannan annoba, kasar Sin za ta ci gaba da nazartar matakan da na sanar yayin bude babban taron lafiya na duniya, za kuma ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka, ta hanyar samar musu da kayayyaki da tura tawagogin masana, da tsara yadda za a sayarwa Afirka kayayyaki daga kasar Sin. Haka kuma kasar Sin za ta fara gina hedkwatar Afirka CDC a wannan shekara, wato kafin lokacin da aka tsara. Kasar Sin za ta yi aiki da Afirka wajen samar da shirin kiwon lafiya da aka amince da shi yayin taron FOCAC na Beijing, da hanzarta gina asibitocin zumunta na Sin da Afirka da hadin gwiwa tsakanin asibitocin sassan biyu. Za kuma mu gina al'umma mai kyakkyawar makomar Sin da Afirka a fannin tsarin kiwon lafiya da zai shafi kowa. Mun yi alkawari cewa, da zarar an samar tare da fara raba allurar rigakafin COVID-19 a kasar Sin, kasashen Afirka ne za su fara amfana.

Na biyu, wajibi ne mu nace wajen karfafa alakar Sin da Afirka. Domin rage tasirin COVID-19, yana da muhimmanci a karfafa hadin gwiwar ziri daya da hanya daya da hanzarta bibiyar sakamakon taron kolin dandalin FOCAC na Beijing. Akwai bukatar a ba da muhimmanci ga hadin gwiwar lafiyar al'umma, sake bude harkokin tattalin arziki da rayuwar jama'a.

A karkashin dandalin FOCAC, kasar Sin za ta soke bashin da take bin wasu gwamnatocin kasashen Afirka da babu kudin ruwa a cikin wadanda ya kamata su biya a karshen shekarar 2020. Ga kasashen na Afirka da COVID-19 ta yiwa mummunar illa kana suke da matsalar kudi, kasar Sin za ta yi aiki da ragowar kasashen duniya, wajen ba su taimakon da ya dace, ta irin wannan hanya har ma za a iya kara wa'adin dakatar da biyan bashin, don taimaka musu fita daga wannan matsala. Muna karfafawa hukumomin kudin kasar Sin gwiwa, su goyi bayan shirin dakatar da biyan bashi na G20 (DSSI) su kuma shirya tattaunawa da kasashen Afirka bisa manufofin kasuwa, don shirya matakan ba da bashi na kasuwanci mai gatanci da kuma tabbaci. Kasar Sin za ta yi aiki da sauran mambobin kungiyar G20, don aiwatar da shirin na DSSI, kuma bisa wannan tsari, ina kira ga G20, da ta taimaka wajen dakatar da biyan bashin ga kasashen da wannan batu ya shafa, ciki har da wadanda ke Afirka.

Kasar Sin tana fatan cewa, kasashen duniya, musamman wadanda suka ci gaba da manyan hukumomin kudi na duniya, za su dauki matakan da suka dace na sokewa Afirka bashin da ake bin su. Kasar Sin za ta yi aiki tare da MDD, WHO da sauran abokan hulda, don taimakawa matakan Afirka na yaki da COVID-19, kuma za ta yi haka ne daidai da muradun Afirka.

A karshe, fatanmu shi ne, taimakawa Afirka ta samu ci gaba mai dorewa. Kasar Sin za ta taimakawa Afirka a kokarin da take yi na raya yankin cinikayya maras shinge na nahiyar da karfafa dunkulewa da karfin masana'antu da samar da kayayyaki. Kasar Sin za ta kara bunkasa alaka da Afirka a fannonin sabbin kasuwanci, kamar cinikayya ta yanar gizo, birane na zamani, da makamashi mai tsafta da fasahar 5G, don inganta ci gaba da farfado da Afirka.

Na uku, wajibi ne mu mayar da hankali wajen karfafa kasancewar bangarori daban-daban. A yayin da ake fama da COVID-19, babban makamin da muke da shi, shi ne hadin kai da taimakon juna. Kasar Sin za ta hada kai da Afirka, wajen tabbatar da jagorancin MDD wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa da goyon bayan WHO wajen ba da muhimmiyar gudummawa a yakin da duniya ke yi da COVID-19, haka kuma muna adawa da nuna wariya da ra'ayi na kashin kai. Abin da muke goyon baya, shi ne daidaito da adalci a duniya.

Na hudu, wajibi ne mu nace wajen ciyar da alakar Sin da Afirka gaba. Duniya tana fuskantar sauye-sauyen da ba ta taba gani a cikin wannan karni ba. Duba da irin sabbin damammaki da kalubalen da muke fuskanta, akwai bukatar hadin gwiwar kut-da kut tsakanin Sin da Afirka, fiye da yadda ake da shi a baya. A banganrena, zan ci gaba da tuntubar dukkanku, abokaina, muddin muna son mu ci gajiyar alakarmu da yadda muke mutunta juna, ya kamata mu rika taimakawa juna kan batutuwa da suka shafi muhimman muradunmu, da fadada manyan muradun kasar Sin da Afirka, da ma kasashe masu tasowa. Idan aka yi haka, za mu iya ciyar da hadin gwiwar Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni gaba.

Abokai

A yayin taron dandalin FOCAC na Beijing, mun amince mu yi aiki tare don gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin Sin da Afirka. Taron kolin musamman na yau tsakanin Sin da Afirka kan yaki da COVID-19, kokarinmu ne na aiwatar da sadaukarwar da muka yi, yayin taron kolin na Beijing, kana mu yi iyakacin kokarinmu, a hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da COVID-19. Na yi amanna cewa, duniya za ta ga bayan wannan annoba, kuma al'ummar Sin da Afirka na da yakinin ganin tarin alheri a nan gaba.(Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China