Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron kolin Sin da Afirka kan hadin gwiwar yaki da COVID-19
2020-06-17 20:48:22        cri
Yau Laraba ne, a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, shugaban na kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron kolin Sin da Afirka na musamman kan hadin gwiwar yaki da COVID-19 da aka bude ta kafar bidiyo.

Kasashen Sin da Afirka ta kudu wadda ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar tarayyar Afirka(AU) da kasar Senegal dake shugabancin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka(FOCAC) ne suka shirya wannan taron cikin hadin gwiwa

Shugabannin kasashen Afirka, ciki har da mambobin babban taron shugabanni da gwamnatocin AU da shugabannin karba-karba na manyan kungiyoyin kasashen nahiyar da shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka(AU) ne suke halartar taron kolin.

Sauran sun hada da babban sakataren MDD da babban darektan hukumar lafiya ta duniya, wadanda ke halartar bikin a matsayin baki na musamman.(Ibrahim´╝ë

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China