Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNiCEF: Kananan yara a Afirka na fuskantar barazana daga COVID-19
2020-06-16 20:53:04        cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF a takaice ya bayyana cewa, kananan yara a Afirka na fuskantar tarin barazana, sakamakon cutar COVID-19.

Asusun wanda ya bayyana haka Talatar nan albarkacin ranar yaran Afirka, ya ce, tasiri na kai tsaye game da wasu manyan tasirin da annobar ta haifar, na barazanar mayar da hannu agogo baya kan nasarorin da yara marasa galibu suka cimma a sassan nahiyar.

A cewar asusun, yayin da takwarorinsu masu galibu ke ci gaba da koyo ta kafar Intanet, a hannu guda kuma, da kyar ake samun daya cikin biyar na magidanta a kasashen gabashi da kudancin nahiyar da ke iya samun Intanet.

Duk da kamarin wannan kalubale, asusun na Unicef yana samun nasara a shiyyar, ciki har da nasarar kaiwa ga mutane miliyan 71 ta hanyar gajeren sakon karta kwana, kan matakan hana yaduwar COVID-19 da yadda za su ci gajiyar hidimomi. Asusun ya kuma taimakawa yara miliyan 10.8 da shirin koyarwa daga gida, baya ga Karin mutane miliyan biyu da aka samar musu kayayyakin wanke hannu da kuma yara da mata miliyan biyu da suka amfana da muhimman kayayyakin kiwon lafiya a cibiyoyin da asusun ke tallafawa(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China