Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasahar saka yadi iri na gargajiya na kabilar Li
2020-06-18 09:56:11        cri

 

 

 

 

 

Malam Chen Daxu ke nan, wanda ya kasance wani malami da ke koyar da fasahar saka yadi irin na gargajiya na kabilar Li da ke lardin Hainan na kasar Sin. Malamin yana da shekaru sama da 30 da haihuwa, amma ya shafe sama da shekaru 20 yana koyon fasahar. Yadda yake sha'awar al'adun gargajiya ya sa ya fara bin tsoffin kauyensu don koyon fasahar saka yadin. Kawo yanzu, ya riga ya zamanto gwani a fannin, har ma dalibai da dama na binsa koyon fasahar. Domin neman kare fasahar saka yadi irin na gargajiya na kabilar Li, makarantu da dama a lardin Hainan suna samar da darrusa na koyar da fasahar, kuma karin matasa na koyon fasahar.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China