Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Ya kamata Sinawa su rayu cikin nishadi
2020-06-15 14:25:48        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ba zai manta da rayuwar da ya yi a tudun Huangtu dake arewacin lardin Shaanxi a lokacin da yake shekaru 15 da haihuwa.

A yayin da Xi Jinping ya zama darektan kwamitin JKS na gundumar Zhengding na lardin Hebei, ya kan hau keke don gudanar da rangadin aiki a kauyuka daban-daban, har ya ratsa kauyuka 200 dake gundumar.

 

Ban da wannan kuma, lokacin da yake rike da mukamin darektan kwamitin JKS na birnin Ningde na lardin Fujian, babu darektan da ya je kauyen Xiadang saboda babu hanya mai kyau, Xi Jinping da tawagarsa sun yi amfani da sandan gora don neman hanyar da ta dace, a karshe sun isa wannan kauye, lamarin da ya sa shi zama darekta na farko da ya kai ziyara a wannan kauye.

Dadin dadawa, lokacin da yake rike da mukamin darektan kwamitin JKS na lardin Zhejiang, Xi Jinping ya rubuta gajeren bayani ga sashin bayanan Zhijiang na jaridar da ake bugawa a ko wace rana ta Zhejiang bisa ayyukan da ya yi a waccan lokaci, inda ya gabatar da ra'ayinsa na bunkasa tattalin arziki ga al'ummar Zhejiang bisa tunani na zamani, da kuma amsa tambayoyin jama'a na yau da kullum.

Watan Yuni na shekarar 2007, a matsayinsa na darektan kwamitin JKS na birnin Shanghai, Xi Jinping ya gabatar da jawabi lokacin da ya ziyarci yankin Huangpu yana mai cewa, hakikanin ci gaban duk wani jami'in gwamnati shi ne samun karbuwa daga jama'a. Ban da wannan kuma, yayin da yake ziyara a kauyen Huamao na garin Fengxiang dake gundumar Zunyi na lardin Guizhou, ya nuna cewa, kimanta nasara ko akasin duk wata manufa, ya dogaro da ko ya samun karbuwa daga jama'a ko a'a.

Bayan barkewar cutar COVID-19 a watan Janairu na shekarar bana, a yayin taron zaunannen mambobin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, Xi ya jaddada cewa, ya kamata sassan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da kuma gwamnatocin kasar sun mai da hankali kan rayuwa da kuma lafiyar jama'a, da kuma sanya ido matuka kan aikin kandagarkin cutar.

Saboda yadda illar da cutar take haifarwa jama'a, ya sa wasu mutane gaza samun kudin shiga, abin da ya sanya su shiga cikin mawuyacin hali, har suka rasa ayyukansu. Don haka, Xi ya jaddada wajibcin tabbatar da zaman rayuwar jama'a lokacin da ya kai ziyara a lardin Ningxia a wannan wata da muke ciki.

 

 

Jimlar da shugaba Xi Jinping ya kan fadi yau da kullum ita ce "Ya dace jama'a su yi rayuwa cikin nishadi", abun da ya bayyana niyyarsa ta cika alkawarinsa da kuma kaunarsa ga jama'a. (Amina Xu)

 

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China