Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Australia ba za ta iya rabuwa da kasar Sin ta fuskar tattalin arziki ba
2020-06-15 14:17:28        cri

Kwanan baya, dandalin tattaunawar gabashin Asiya na kasar Australia da jami'ar kimiyya da fassaha ta kasar sun gabatar da rahoton nazarinsu, inda suke ganin cewa, rabuwar Australia da kasar Sin ta fuskar tattalin arziki ba zai amfana mata ko kadan ba. Dukkan kasashen duniya za su samu karfin bunkasuwa sakamakon yadda kasar Sin ta samu nasarar yaki da annobar cutar numfashi ta COVID-19 cikin gajeren lokaci da kuma raya tattalin arzikinta yadda ya kamata.

A 'yan kwanakin baya, Sin da Australia sun gamu da matsala a fannin raya huldar da ke tsakaninsu. Wasu 'yan siyasan Australia da kafofin yada labaru na kasar sun yi shelar cewa, Australia tana dogaro da kasar Sin fiye da kima ta fuskar tattalin arziki, a don haka, kamata ya yi ta raba gari da kasar Sin. Dangane da wannan, kwalejin nazarin hulda tsakanin kasashen 2 ta jami'ar kimiyya da fasaha ta Australia ya gabatar da rahoton nazari, inda ya ruwaito alkaluman da ma'aikatar harkokin waje da ciniki ta Australia da fitar, wadanda ke nuna cewa, a shekaru 10 da suka wuce, jimillar kudin da Australia ta samu a fannin sayar da kaya a ketare ta karu da dalar Austrlia biliyan 180 a kowce shekara, kuma kashi 60 cikin kashi dari ne na ciniki da kasar Sin ne. Idan har aka tilasta wa Australia ta raba gari da kasar Sin ta fuskar ciniki, hakan na iya rage kudin shigar da 'yan Austrlia ke samu da ma damar samun aikin yi. Dakta James Laurenceson, daya daga cikin wadanda suka rubuta rahoton, kuma shugaban kwalejin nazarin hulda tsakanin Asutralia da Sin ya yi bayani cewa, "Bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin tana da matukar muhimmanci gare ta da ma duk duniya baki daya. A shekaru fiye da 10 da suka wuce, kasar Sin ta ba da gudummawa kashi 1 bisa uku na ci gaban tattalin arzikin duniya. Ko shakka babu kasar Austrlia ma ta ci gajiya, kana kuma za mu ci gaba da cin gajiya. Alkaluman tattalin arzikin kasar Sin sun nuna cewa, yanzu kasar Sin na kokarin fitar da kanta daga radadin annobar."

Madam Jane Golley, wata masanar ilmin tattalin arziki a jami'ar kasar Australia, wadda ta shafe shekaru 25 tana nazarin tattalin arzikin kasar Sin tana ganin cewa, tattalin arzikin Australia ya dogara ne da kasar Sin, in ba haka ba, ba ta iya samun ci gaba cikin shekaru da dama da suka wuce ba. Sakamakon yadda kasar Sin ta fita daga radadin annobar ta COVID-19, ya sa Australia ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin, in ba haka ba, ba za ta iya tabbatar da bunkasar tattalin arzikinta bayan annobar ba. Masanar ta ce, "'Yan kasuwan Australia da ma daukacin 'yan kasar, na cin gajiyar ci gaban kasar Sin a shekarun da suka wuce. Amma wasu kafofin yada labaru da masana sun yi ta yin surutun cewa, ko Australia na dogaro da kasar Sin fiye da kima ko a'a, ko ya fi kyau Australia ta raya tattalin arziki ta hanyoyi daban daban, musamman ma a lokacin da babbar kawarta kasar Amurka da kuma babbar abokiyar cinikinta kasar Sin suka gamu da matsala wajen raya huldar da ke tsakaninsu. Wane mataki Australia ya dace ta dauka? Idan har ta zabi hanyar raya tattalin arziki ta hanyoyi daban daban, tabbas za ta fuskanci kalubale da dama. Shaidu da alkaluma sun shaida cewa, tattalin arzikin kasar Sin mai karfi yana da matukar muhimmanci ga Australia, musamman ma a fannonin ciniki da zuba jari. Ko da yake annobar ta COVID-19 ta kawo illa ga tattalin arzikin kasar Sin, amma za ta samar wa Australia kyakkyawar dama wajen samun ci gaba mai dorewa."

Kwanan baya, dandalin tattaunawar gabashin Asiya na Australia ya gabatar da wani bayani mai suna "raba tattalin arzikin Australia da na kasar Sin zai sadaukatar da abubuwa da yawa", inda ya yi nuni da cewa, huldar da ke tsakanin Australia da Sin ta fuskar tattalin arziki da ciniki da suka rika ciyar da ita gaba, ta dace da muradun kasashen 2 duka. Dangane da wannan, dakta James Laurenceson yana ganin cewa, kamata ya yi Australia ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin. Kasar Sin tana bin hanyar kirkire-kirkire, wadda za ta amfana wa Australia. "Kasar Sin ta tsara wani shirin raya tattalin arziki yadda ya kamata. Alal misali, ta fahimci cewa, idan ta son kara kudin shigar jama'arta, to, dole ne a kara azama kan ci gaban kimiyya da fasaha da kara ingancin aiki. Hanyar da kasar Sin ta bi wajen raya kasa a baya, ba za ta yi nasara ba. Masanan tattalin arziki na kasar Sin, su ma sun gane haka sosai. Muddin a hada kai da kasar Sin sosai, hakika kasashen duniya za su ci gajiyar ci gaban Sin, ciki had da Australia. Kana kuma bunkasar tattalin arzikin duniya za ta amfana wa kasar Sin. Idan kasar Sin ta tsara shirinta na raya tattalin arziki yadda ya kamata, babu tantama tattalin arzikin duniya baki daya zai farfado." (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China