Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
AU ta yabawa gudunmawar da Sin ke baiwa Afrika a yaki da COVID-19
2020-06-14 17:42:18        cri
Kungiyar tarayyar Afrika AU ta bayyana godiyarta bisa muhimmiyar gudunmowar da kasar Sin ke baiwa kasashen Afrika wajen yaki da annobar COVID-19.

Wannan sakon murna na kunshe ne cikin sanarwar bayan taron da aka gudanar ta kafar bidiyo na shugabannin majalisar kungiyar gami da shugabannin majalisar tattalin arziki na kungiyar.

A cewar sanarwar, shugabannin kasashe da hukumomin gwamnati sun yabawa muhimmiyar gudunmowar da jamhuriyar jama'ar kasar Sin take bayarwa game da wannan yunkuri, wanda ya hada da ware wani kaso mai yawa na kayayyakin da masana'antun kasar ke sarrafawa domin samar da kayayyakin gwaje gwajen cutar miliyan 30, da na'urar taimakawa numfashi 10,000, da takunkumin rufe fuska miliyan 80 cikin kowane wata ga nahiyar.

A lokacin taron, shugabannin kasashen mambobin AU sun amince da kaddamar da kafa gidauniyar samar da kayayyakin kiwon lafiya ta kasashen Afrika da nufin kula da aikin samarwa da rarraba kayayyakin kiwon lafiyar ga mambobin kasashen na AU.

A cewar sanarwar bayan taron, AU ta bayyana aniyar yin hadin gwiwa da kasashen duniya da dama da suka hada da Sin, Canada, Netherlands, Koriya ta kudu, da Faransa domin aikin samar da muhimman kayayyakin kiwon lafiyar da ake bukata kamar na'urar taimakawa numfashi, da kayayyakin bada kariya, da na gwaje gwaje wadanda nahiyar ke bukata cikin gaggawa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China