Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu karuwar yawan mutanen da suka bada gudummawar jini ba tare da riba ba a kasar Sin cikin shekaru 22 a jere
2020-06-14 17:35:28        cri

 

Yau ce ranar masu bada gudummawar jini ta duniya karo na 17, babban taken ranar ta bana shi ne "samar da jini mai tsaro, domin ceto rayuka". Bisa kididdigar da kwamitin lafiyar kasar Sin ya yi, an ce, masu bada gudummawar jini a nan kasar Sin sun karu daga sau dubu 328 a shekarar 1998 zuwa miliyan 15.63 a shekarar 2019, yawan masu bada jini ba tare da samu riba ba, da yawan jini da aka dauka duka sun karu a cikin shekaru 22 a jere. A 'yan kwanakin da suka gabata, masu aikin sa kai a wurare daban daban na kasar suna sa himma wajen bada gudummawar jini ba tare da samun riba ba, domin ceto mutane masu fama da jinya.

A kwanan nan, a wannan dakin bada jini dake gundumar Changxing ta lardin Zhejiang, akwai mazauna wurin sama da 20 a kowace rana sun zo nan don bada jini.

 

 

A wannan wajen mai aikin sa kai Shen Yueyun yana bada jini sau biyu a kowace shekara tun daga shekarar 2003, jimilar jinin da ya bayar ya wuce 11200ml.

 

 

Shugaban tashar samar da jini na cibiyar birnin Zhaotong na lardin Yunnan Bi Cheng'en ya ce, mun yi bincike kan samfurin jinin da aka bayar don tabbatar da ko akwai masu dauke da cutar COVID-19, kana mun gudanar da aikin kashe kwayar cutar kan jinin.

 

 

A daren ranar 12 ga wata, an yi wani biki don girmama masu bada gudummawar jini ba tare da samun riba ba a wani jirgin ruwa na yawon shakatawa a kogin Xin'an dake dutsen Huangshan na lardin Anhui, inda masu aikin sa kai sama da 30 suka samu furanni da tafin da aka yi musu.

 

 

Li Xin' wata mai aikin sa kai na bada jini ba tare da samun riba ba, ta ce, ina amfani da jinina don taimakawa sauran masu bukata, a ganina wannan aiki na da ma'ana sosai, ina fatan ganin mutane masu yawa za su shiga wannan aikin namu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China