Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afrika 43 na cikin dokar kulle kan iyakokinsu yayin da adadin yawan masu cutar COVID-19 ya zarce 225,000 a fadin nahiyar
2020-06-14 16:42:11        cri
Yayin da yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ya kai 225,105 ya zuwa ranar Asabar a fadin nahiyar Afrika, a yanzu haka kasashe 43 a Afrika sun tsaurara dokar kulle kan iyakokinsu saboda da bazuwar annobar.

Jimillar mutanen da annobar ta hallaka ya kai 6,040, yayin da mutane 102,846 sun warke daga cutar, kamar yadda alkaluman baya bayan nan na hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta bayyana.

Kasashen Afrika da annobar COVID-19 tafi yin kamari sun hada da Afrika ta kudu, Masar, Morocco, Djibouti, Najeriya, da Algeria, kamar yadda hukumar lafiyar ta AU ta sanar.

Baya ga kasashen 43 dake karkashin dokar tsaurara rufe kan iyakokinsu, Afrika CDC ta kara da cewa, an kafa dokar hana fita da dare a kasashen Afrika 35 a kokarin dakile yaduwar annobar.

A cewar Afrika CDC, dukkan kasashen Afrika 54 suna aiwatar da dokar takaita taruwar jama'a, kana wasu kasashen nahiyar 38 sun kafa dokar rufe makarantu a fadin kasashen, da kafa dokar kayyade ziyartar gidajen yari da asibitoci a kasashen Afrika 20.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China