Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Likitocin kasar Sin sun more dabarun jiyyar masu fama da cutar COVID-19 da takwarorinsu na Brazil
2020-06-11 14:36:52        cri

Kwanan baya, likitocin asibiti na uku na jami'ar Peking, da takwarorinsu na kasar Brazil sun shiga wani shirin da CMG ta gabatar a kan Intenat kai tsaye mai jigon "Dakin jiyyar COVID 19 na kasa da kasa", inda likitocin kasar Sin suka more dabarun jiyyar masu dauke da wannan cuta.

Shugabar asibitin, kana mai jagorancin tawagar likitocin jami'ar Peking karkashin tallafin lardin Hubei, kwararriya Qiao Jie ta ce, asibitin ya tura masu aikin jiyya fiye da 400 zuwa lardin Hubei, inda suka kwashe kwanaki sama da 70 suna kokarin yakar cutar, inda suka samun dabaru da fasahohi masu dumbin yawa, a fannin kandagarki, da gwaje-gwaje, da bincike, da kuma jiyyar masu dauke da cutar. A cewarta, more wadannan dabaru da fasahohi, nauyi ne dake wuyansu, kuma aiki ne na wajibi da suka yi.

Ya zuwa yanzu, cutar ta kara tsananta a Brazil. Bisa kididdigar da hukumar kiwo lafiya ta kasar ta bayar, an ce, ya zuwa karfe 6 na yammacin ranar 10 ga wata agogon wurin, yawan mutane da suka kamu da cutar ya kai 772,416, yayin da yawan mamata ya kai 39680.

Darektan sashin ICU na kamfanin jiyya na nahiyar Amurka na kasar Brazil Victor Cravo ya ce, yawan mamata daga cikin mutanen da suke cikin halin rai kwakwai mutum kwakwai ya kai kaso 70 bisa dari a asibitocin kasar. A asibitoci masu zaman kansu kuwa wannan adadi ya kai kaso 56 bisa dari, yana mai fatan dabarun kasar Sin za su taimakawa kasar wajen rage yawan mamata.

Babbar likita ta asibiti na uku na jami'ar Peking Li Shu ta ce, an samu mamata masu yawa a farkon barkewar wannan cutar a kasar Sin, kuma yawan mamata a sashen ICU ya kai kaso 52%, saboda masu kamuwa da cutar masu dimbin yawa suna jiran damar shiga asibiti, amma a waccan lokaci an gaza samun isassun gadaje, da kayayyakin jiyya, da kayayyakin kandagarki. A wani bangaren kuwa, halin wadansu masu dauke da cutar ya kara tsananta cikin sauri, wanda hakan ya haddasa yawan mamata.

Li Shu ta ce, bayan an tattara karfin daukacin kasar don tallafawa birnin Wuhan, a wani lokaci an taba samun na'urori masu taimakawa numfashi wato ECMO guda 30 a dakin da ta ba da jiyya, saboda haka, karfin ba da jiyya ya karu sosai.

A cikin wannan shiri mai tsawon awa daya, likitocin bangarorin biyu sun tattauna kan ma'aunin cire ECMO, da kuma wasu abubuwa da ya kamata an lura da su wajen amfani da ECMO, da yadda za a yi amfani da magungunan yakar kwayar cutar da dai sauran matsaloli. Ban da wannan kuma, likitocin kasar Sin sun amsa tambayoyin da takwarorinsu na Brazil suka gabatar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China