Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kowa Ya Ga Yadda Kasar Sin Ta Ba Da Gudummawa Wajen Hada Kan Kasa Da Kasa Ta Fuskar Yaki Da Annobar COVID-19
2020-06-09 20:53:10        cri
Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da takardar bayani kan matakan da ta dauka wajen dakile da kandagarkin annobar cutar numfashi ta COVID-19, inda aka yi karin bayani kan tunanin kasar Sin dangane da hada kan duniya wajen yaki da annobar da matakanta da kuma kiran da ta yi. Takardar bayanin ya nuna cewa, kasar Sin ta dauki hakikanin matakai domin aiwatar da tunanin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan 'yan Adam, tana kuma sauke nauyi bisa wuyanta a matsayinta na babbar kasa, wadda take hadin gwiwa kafada da kafada da kasashen duniya wajen yaki da annobar. An lura da cewa, an ambato kalmar "hadin-gwiwa" sau da dama a cikin wannan takardar bayani, inda aka rubuta alkaluma da shaidu na hakika masu dimbin yawa dangane da wahalhalun da jama'ar Sin suka sha wajen yaki da annobar, da kuma yadda kasar Sin ta hada kai da kasashen duniya wajen yaki da annobar ba tare da bata lokaci ba. Alal misali, sanar da bayanai kan lokaci, samar da kyawawan fasahohin yaki da annobar, ba da tallafin jin kai gwargwadon karfinta, sayar da kayayyakin yaki da annobar yadda ya kamata, yin hadin gwiwa da mu'amala a tsakaninta da kasashen duniya ta fuskar nazarin kimiyya da dai sauransu.

A daidai lokacin da annobar ta COVID-19 take ci gaba da yaduwa a duniya, takardar bayanin ta jaddada cewa, dakile da kandagarkin annobar ta COVID-19 a duniya wani muhimmin aiki ne na tabbatar da tsaron lafiyar al'ummar duniya, kiyaye lafiyar 'yan Adam, tabbatar da wadata da ci gaban duniya da tabbatar da adalci a duniya.

A cikin wannan muhimmin aiki mai nasaba da makomar dan Adam, kiran kasar Sin da kuma matakan da ta dauka, za su ba da gudummawa gwargwadon karfinta wajen samun nasarar yaki da annobar. A don haka, ya kamata 'yan siyasan kasashen yammacin duniya, wadanda suke kokarin dora wa wasu laifi a ko da yaushe, su kai zuciya nesa, su taimakawa jama'arsu da ma kasashen duniya wajen yaki da annobar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China