Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin Sin ta samar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya ga rundunonin sojojin kasashe 20
2020-06-05 21:16:35        cri

 

 

 

 

Don tabbatar da tunanin gina kyakkyawar makomar bil Adama ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin, ta samar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya dake kunshe da kayan ba da kariya, da kayan rufe baki da hanci da ake amfani da su a asibiti da sauransu, ga rundunonin sojojin kasashe 20, bisa rokon da suka yi.

An gabatar da kayayyakin ne ta jiragen saman sojojin saman kasar, tsakanin ranar 2 zuwa 5 ga watan nan, bayan da suka samu amincewa daga kwamitin aikin soja na kwamitin tsakiya na JKS.

Wadannan kasashe sun hada Habasha, da Mozambique, da Tunisiya, da Angola, da Masar, da Morroco, da Tanzaniya, da Kongo(Brazzaville), da Kongo(Kimshasa), da Equatorial Guinea, da Saliyo. Sauran sun hada da Zimbabwe, da Zambiya, da Kamaru, da Ruwanda, da Agentina, da Laos da Kambodia, da Saudi Arabia, da Bangladesh.

Bil Adama suna da makoma guda, don haka ya dace a hada kai domin ganin bayan annoba, kuma rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin za ta ci gaba da kara karfafa hadin gwiwa dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, domin kiyaye tsaron kiwon lafiyar jama'a a fadin duniya.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China