Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda kwararrun likitocin kasar Sin suka taimaka wajen yaki da cutar COVID-19 a kasar Zimbabwe
2020-06-05 14:13:08        cri

Daga ranar 11 zuwa 25 ga watan Mayun da ya gabata, wata tawagar masana ilimin aikin likitanci ta kasar Sin ta gudanar da wasu ayyuka a kasar Zimbabwe, don taimakawa kokarin kasar na neman ganin banyan cutar COVID-19.

Wannan tawagar masana ilimi aikin likitanci ta kasar Sin, da aka tura ta zuwa kasar Zimbabwe, ta kunshi kwararrun likitoci 12, wadanda suka kware a fannonin kula da masu kamuwa da cutar numfashi, da cuta mai yaduwa, da jinyar masu tsananancin rashin lafiya , da dai makamantansu. Wadannan kwararrun likitoci sun bayyanawa wakilinmu yadda suke gudanar da ayyukansu a kasar Zimbabwe.

"Sunana Hu Chengping, ni ce shugaban tawagar masana ilimin jinyar masu kamuwa da cutar COVID-19 ta lardin Hunan na kasar Sin."

Wannan kwararriyar likita na kasar Sin ya ce, wani asibitin da aka kebe domin kwantar da majiyyata masu kamuwa da cutar COVID-19 dake birnin Harare na kasar Zimbabwe, yana fama da matsalar rashin kayayyakin kandagarkin cuta, da sauran na'urorin kula da majinyata da ake bukata. Wannan yanayi, ya kara wa mutanen da suka harbu da cutar damuwa matuka.

Sai dai wani abu mai kyau shi ne, kamfanonin kasar Sin dake gudanar da harkokinsu a kasar Zimbabwe sun taimaka a wannan fanni, inda suka taimaka wajen gyara fasalin asibitin, tare da samar da dimbin kayayyakin kandagarkin cututtuka ga gwamnatin kasar Zimbabwe. Wadannan aikace-aikace na kirki sun burge madam Hu sosai, ta ce a matsayinta na Basiniya, tana alfahari da irin gudunmowar da wasu 'yan kasarsa suka samar ga aikin dakile cutar COVID-19 a kasashen Afirka.

Madam Hu ta kuma bayyana yadda aka yi musayar ra'ayi tsakaninsu da takwarorinsu na kasar Zimbabwe, inda a yayin wani taron karawa juna sani, wani masanin ilimin hana yaduwar cututtuka mai suna Manangazira, ya ce an yi ta daidaita tsarin kandagarkin cutar COVID-19 a birnin Harare har karo 4, bisa fasahohin da kasar Sin ta raba ma kasashe daban daban. Mista Hu ya ce wani abu mai burgewa shi ne, yadda likitocin kasar Zimbabwe ke kokarin aiwatar da matakai na hana yaduwar cuta, gami da jinyar masu kamuwa da cuta, duk da cewa ba su da isassun kayayyakin da suke bukata.

A nata bangare, madam Sun Qianlai, wata likita mai kula da aikin hana yaduwar cututtuka, ita ma ta bayyana wa wakilinmu abun da ya burge ta.

"Ganin cewa, a wannan mako ya kamata mu ziyarci wurare daban daban, don haka kusan kowace rana muna tafiya da abincin da za mu ci a tsakar rana yayin da muke cikin mota, har ma da direbanmu. Amma na kan ga abinci kadan yake ci, sa'an nan ya ajiye shi. Daga baya mun gano cewa, yana cin abinci sau daya ne kawai a rana, sa'an yana tsimin abinci domin iyalansa dake gida. "

Daga bisani, Peng Yue, wata kwararriyar likita mai kula da majiyyata wadanda yanayinsu ke da tsanani, ta gaya mana wani abun da ta ji yayin da take rangadi a wani asibiti.

"A wani asibitin da muka ziyarta, jami'ai da likitocin wurin sun karbe mu da hannu biyu-biyu. Sa'an nan duk lokacin da ake shirin gudanar da wani taro, dukkamu kan rera wani take. Da farko dukkanmu mu kan tashi tsaye, sa'an nan abokan aikinmu na kasar Zimbabwe sai su rera taken kasarsu, daba baya mu ma sai mu rera taken kasar Sin. Wannan shi ne karo na farko da na rera taken kasar Sin a wani wuri da ba na kasarmu ba. Yayin da na ji taken da muka rera, gaskiya muryar ta burge ni matuka, sai da na zub da hawaye. Saboda ina matukar alfahari da kasarmu, kan yadda muke kokarin taimakawa sauran kasashe, tare da samun yabo da jinjina da girmamawa."

Duk wadannan kwararrun masana ilimin aikin likitanci na kasar Sin sun shaida yadda jama'ar Zimbabwe da ta kasar Sin suke kokarin hadin gwiwa da juna, don neman kawo karshen cutar da COVID-19, da farfado da tattalin arziki, da zaman rayuwar jama'a na yau da kullum. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China