Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daliban makarantun firamare da na midil da na sakandare sun soma komawa makarantu daya bayan daya a nan birnin Beijing
2020-06-04 15:39:28        cri


Bisa kyautattuwar halin da ake ciki na dakile annobar COVID-19 a nan kasar Sin, gidajen renon yara masu yawa na shirin sake bude kofa daya bayan daya. Amma, kamar yadda kowa ya sani, yara ba su da karfin garkuwar jiki sosai wajen hanasu kamuwa da cuta, don haka yaya za a kiyaye tsaron lafiyarsu bayan sun komo gidan renon yara, wannan ya kasance wani batu mai muhimmanci kwarai a gaban duk al'ummar kasar. A cikin shirinmu na yau, zamu kawo muku wani bayani game da haka.

A hakika dai, ban da cutar COVID-19, haka nan kuma yara na fuskantar wasu cututtuka masu yaduwa da dama, kamar yaduwa cutar ta hannu, kafa da baki, yaduwar cutar gyambon makogwaro na kuraje da dai sauransu, musamman ma a lokacin zafi. Domin kiyaye lafiyar yara, lallai gidajen renon yara da yawa na kasar Sin sun dauki matakai masu yawa.

Binciken safiya, muhimmin ma'aunin kula da lafiya ne a gidajen renon yara. Babban dalilin binciken safe shine don hana yara kawo cututtukan dake haifar da haɗari da kayan haɗari a cikin gidajen renon yara, wanda ke da ma'anar kiyaye lafiya da tabbatar da tsaro.

Hanya ta gargajiya da ake bi wajen yin binciken safiya ita ce malamai masu kula da lafiya su duba halin da yara ke ciki. Yanzu, wasu gidajen renon yara na zamani sun fara amfani da sabuwar fasaha don taimakawa malamai wajen yin binciken. Wato mutum-mutumin inji na binciken lafiya da safe.

Ga misali, akwai irin mutum-mutumin inji mai saurin bincike lafiya kirar kamfanin Suzhou Vokelec. To, yaya yake gudanar da aikinsa?

Shugaban sashen nazari na kamfanin mista Dong ya bayyana cewa,

"'Yaran suna sa hannayensu a cikin mutum-mutumin jinji, su kuma sanya kumatu a saman ramin, sannan su bude bakinsu. Bayan dakika 3, za'a sami sakamako."

Mista Don ya kara da cewa, wannan mutum-mutumin inji na iya kammala aikin bincike kan zazzabi na jiki, baki, hannaye, da idanu a cikin dakika 3. Yana iya gano cututtukan yau da kullun na yara sama da 20, kamar cututtukan hannu, ƙafa da bakin, jan idanu da dai sauransu.

 

Mista Dong ya bayyana cewa,

"Idan ƙararrawa ta bayyana matsala, to malaman kula da lafiya zasu sake tabbatarwa. Hakan aka kara ingancin dubawa safe da kuma nisantar sakaci a ciki.

Mista Dong ya ce, irin mutum-mutumin inji yana aiki ne domin yara kanana, don haka sun yi tunani sosai kan salonsa a yayin da suke tsarawa.

"Domin sanya yara su yi sha'awa kan binciken lafiya d safe, mun tsara salo irin na muhimman mutane da suka fito daga fim din na Minions, kuma kamar yadda kuke gani, mun zabi launuka guda biyu, wadanda yara suka fi so, wato launin rawaya da yara maza ke so da na ruwan hoda da yara mata ke so."

Mista Dong ya kara bayyana cewa, mutum-mutumin inji da suka tsara yana da cikakkiyar halayyar hoto mai ƙarfin hankali da ƙarfin gano zafin jiki, kuma yana iya kammala shigar da yara nan take, gwajin zazzabi na jiki, nazarin herpes, hannu a cikin dakika 3 kawai. Ana iya tura sakamakon binciken safiya ga iyayen yara akan dandalin sada zumunci na WeChat, don taimakawa shugabanni da malamai na gidajen renon yara su aiwatar da aikin binciken safe da kuma aikin kula da cututtuka yadda ya kamata kamar yadda ma'aikatar lafiya ke buƙata.

Binciken safiya yana kan matsayi mai mahimmanci a cikin aikin gidajen renon yara. Ba wai kawai yana hana yaduwar cututtuka bane, har ma yana iya kawar da boyayyen haɗarin. Shi babban ma'aunin lafiya ne da aka dauka don tabbatar da lafiyar da tsaron yara. Mutum-mutumin inji na binciken lafiya da safe ya inganta aikin nan, idan aka kwatanta da binciken gargajiya na yau da kullun, mutum-mutumin inji na gudanar da aikin ne bisa ma'auni mafi tsanani, za a yi amfani da mutum-mutumin inji don gudanar da wannan aiki amma ba 'yan adam ne za su yi ba a dukkan fannoni.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China