Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Murna ta koma ciki dangane da ganin bayan cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo
2020-06-02 17:11:01        cri
Murna ta koma ciki a kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, inda a jiya Litinin hukumomi suka tabbatar da sake barkewar cutar Ebola a Mbandaka, babban birnin lardin Equateur dake arewa maso yammacin kasar ta yankin tsakiyar Afrika. A baya, kasar ta shirya ayyana kawo karshen cutar Ebola, sai kwatsam aka samu mutuwar mutane 5 tsakanin ranekun 18 zuwa 30 ga watan Mayu, amma ba a kai ga tabbatar da musababbin mutuwarsu ba sai a jiya Litinin. Akwai kuma wasu mutane 4 da suka yi mu'amala da masu cutar, da yanzu haka aka killace, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana.

Wannan sabon yanayi, ya sake mayar da hannun agogo baya dangane da ci gaban da aka samu a kasar mai fama da rikici, dangane da yakar cutar Ebola mai kisa. Duk da cewa an samu nasarar fatattakar cutar Ebola a galibin kasashen da cutar ta barke a nahiyar Afrika, matsalar ta ki ci ta ki cinyewa a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. Ya zuwa 24 ga watan Mayun da ya gabata, cutar ta harbi mutane 3,317, sannan ta yi sanadin rayuka 2,134 .

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ta kuma tsinci kanta cikin matsanancin yanayi da duniya ke fama da shi na barkewar annobar COVID-19, inda zuwa ranar 31 ga watan Mayu, aka tabbatar da bullarta a larduna 7 na kasar, da jimilar mutane 3,070 da suka kamu da ita. Har ila yau, kasar ta kasance wadda cutar kyanda ta fi kamari a duniya.

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, kasa ce mai arzikin albarkatu, sai dai a baya-bayan nan kasar ta na fama da rikice-rikice da rashin ababen more rayuwa da sauran wasu matsaloli.

Wadannan matsaloli kuma su ne ke kara fafatawa da kasar a kokarin da take na ganin bayan cutar Ebola. Misali, ayyukan masu dauke da makamai kan hana masu ayyukan agaji isa wurare masu nisa dake fama da cutar. Baya ga haka, a wasu lokutan, wadannan 'yan bindiga kan kai hare-hare musammam kan ma'aikatan jinya dake sadaukar da rayukansu wajen ganin sun yaki wannan cuta.

Kowacce matsala kan fara ne daga cikin gida, haka zalika mafita ko maganinta na nan a cikin gida. Ya zama wajibi bangarori masu ruwa da tsaki a kasar su ajiye bambancin dake tsakaninsu su hada hannu su ceto kasarsu daga matsalolin da take fuskanta. Ba zai yiyu a ce ana tufka ana warwara ba. Kana wajibi ne su amsa kiran duniya na tsagaita bude wuta domin shawo kan cututtukan da suka addabi kasar. Kiwon lafiya ya shafe duk wani sabani ko bambanci, domin cuta mai saurin yaduwa irin Ebola ko COVID-19, ba su san bangarori masu adawa da juna ba.

Al'ummar kasar da kansu na da muhimmiyar rawar takawa wajen dakile wannan cuta. Ya kamata su dauki batun kula da lafiyarsu da muhimmanci, domin idan suka yi haka, ba kansu kadai za su kare ba, har ma da sauran al'ummar duniya, musamman kasancewar garin Mbandaka da cutar ta barke a wannan karo, matsayin cibiyar harkokin kasuwanci. Har ila yau, kamata ya yi su kauracewa cin dangin dabbobin dake dauke da wannan cuta, bisa la'akari da rahotannin dake cewa, mazauna garin na yawan cin namun daji. Sannan akwai bukatar su dauki matakan kariya da shawarwarin masana da muhimmanci, domin masu iya magana kan ce, zaman lafiya ya fi zama dan sarki.

Ban da wannan, kasashen duniya ma na da gudunmuwar da ya kamata su bayar, bisa la'akari da yadda nahiyar Afrika ke fama da rashin ingantaccen tsarin kiwon lafiya da sauran ababen ci gaba. Bai kamata a ce taimako ya zama bisa wani sharadi ko moriya ba, domin Jamhuriyar Deokradiyyar Congo na bukatar taimako gaya. Dukkan bil adama 'yan uwan juna ne, kuma rai da lafiya su ne abubuwa mafi muhimmanci ga bil adama. Ya kamata kasashe masu karfin tattalin arziki da gogewa da ci gaba, su kara kai wa wannan kasar ta tsakiyar Afrika dauki domin fatattakar cutar baki daya, duba da yadda taki ci taki cinyewa. Kana idan ta ci gaba da yaduwa, to babu wata kasa da za ta tsira. Al'ummar duniya ba su cancanci kara shiga matsanancin yanayin da suka shiga a lokacin da cututukan Ebola da COVID-19 suka fara bulla ba. (Faeza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China