Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dukkan bangarorin Hong Kong sun goyi bayan matakin da NPC ta dauka kan batun kafa dokar Hong Kong
2020-06-02 14:55:05        cri
Bayan shudewar wasu kwanaki, bangarori da dama a Hong Kong, sun goyi bayan matakin da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin wato NPC ta dauka game da shigar da batun yankin musamman na Hong Kong.

Da yammacin ranar 1 ga watan Yuni, masu gabatar da bayanai suka mika sakamakon da aka tattara ga ofishin yin mu'amala tsakanin gwamnatin tsakiya da gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, da nufin gabatar da sakamakon ga gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta hanyar ofishin mu'amala na gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake yankin musamman na Hong Kong inda sakamakon ya kunshi batun nuna sha'awar da al'ummar Hong Kong suka yi wajen goyon bayan mahukuntan Hong Kong domin aiwatar da dokar kyautata tsaron al'umma.

Luo Huining, daraktan ofishin mu'amala na gwamnatin tsakiyar kasar Sin dake yankin musamman na Hong Kong, ya ce a cikin kwanaki 8 ke nan, sama da mutane miliyan 2.92 sun fito kan tituna don yin rijista kana sun sa hannu a shafin intanet, wanda hakan ya nuna cikakkiyar sha'awar da mutane suka nuna goyon bayan al'ummar Hong Kong da kuma nuna cikakkiyar amincewa da dokar tsaron al'umma ta yankin musamman na Hong Kong wannan shi ne hakikanin abin da mutane ke son a baiwa muhimmanci.

A wannan rana, shugabannin jami'o'i biyar a Hong Kong sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka bayyana cikakken goyon bayansu kan manufar kasa daya, amma tsarin mulki biyu, tare da bayyana gamsuwarsu game da samar da daftarin dokar tsaron al'umma.

Wu Qiubei, wakilin jama'a ta majalisar kafa dokokin kasar Sin dake wakiltar yankin musamman na Hongkong, ya ce al'ummar yankin Hong Kong sun gaji da tashin hankalin da suka fuskanta cikin shekara daya da ta gabata, don haka jama'ar yankin masu yawa suna bukatar a kafa dokar kandagarkin wannan tashe-tashen hankula a yankin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China