Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bullo da babban shirin gina tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci a tsibirin Hainan
2020-06-02 12:33:56        cri

Kwanan nan, kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da kuma majalisar gudanarwa ta kasar, sun wallafa wani babban shiri kan gina tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci a tsibirin Hainan dake kudancin kasar Sin, inda aka tsara ayyukan gina ta daga dukkanin fannoni. To, yaya kasar Sin za ta gina wannan tasha a Hainan? Mene ne amfaninta? Ta yaya za'a bullo da tsare-tsare da manufofi a matakai daban-daban a tashar?

Babban shirin gina tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci ya shafi fadin tsibirin Hainan baki daya, inda ya yi bayani kan yadda za'a raya tashar daga dukkanin fannoni kuma bisa matakai daban-daban. Wasu kwararru na ganin cewa, ci gaban kasar Sin na bukatar fadada bude kofarta ga kasashen waje. Kamar lokacin da aka fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, an raya birnin Shenzhen har ya zama yankin musamman ta fannin tattalin arziki, a sabon zamanin da muke ciki yanzu, akwai bukatar gina tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci a tsibirin Hainan, don ta zamanto wani babban misalin kasar Sin a fannin bude kofa ga kasashen waje. Dangane da batun, babban masanin tattalin arziki daga cibiyar mu'amalar harkokin tattalin arzikin kasa da kasa dake kasar Sin, Zhang Yansheng ya bayyana cewa:

"Yanzu tsibirin Hainan ya zama wani sabon zarafi a gare mu, wanda ya kasance tamkar wata sabuwar taga ko gada dake janyo masu basira da ingantattun abubuwa, da cibiyoyin yin kirkire-kirkire daga kasa da kasa, don su shigo kasar ta Sin, ta yadda harkokin kimiyya da fasaha da sana'o'in kirkike-kirkire na kasar za su bunkasa, kana za'a iya zamanintar da manufofi da ka'idoji na kasar. Dadin dadawa, raya tashar dake tsibirin Hainan zai iya hada tattalin arzikin kasar Sin da na fadin duniya waje guda."

Babban shirin ya zayyana cewa, burin gina tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci a tsibirin Hainan shi ne, zuwa shekara ta 2025, yadda aka kafa tsarin manufofin raya tashar cinikayya ta ruwa zai saukaka matakan cinikayya da na zuba jari. Sa'an nan ya zuwa shekara ta 2035, tashar za ta zama sabon sashin raya tattalin arziki dake bude kofa ga kasashen waje. Kana, ya zuwa tsakiyar wannan karnin da muke ciki, za'a kammala aikin gina babbar tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci wadda za ta taka muhimmiyar rawa a duk fadin duniya.

Domin cimma wadannan muradun, shirin da aka bullo da shi ya kunshi wasu muhimman matakan yin kirkire-kirkire, ciki har da saukaka matakan cinikayya, da na zuba jari, da saukaka musanyar kudade tsakanin kasa da kasa, da saukaka zirga-zirgar jama'a da na kayayyaki. A ganin kwararru da masana, irin wadannan matakan da aka sanar, ba'a taba ganin irinsu ba a tarihi. A nasa bangaren, mataimakin shugaban cibiyar nazarin ilimin zamantakewar al'umma ta kasar Sin, Gao Peiyong ya ce:

"Ya kamata mu fahimci matakan kawo saukin da kyau. A wani bangaren, ya kamata mu sakar musu mara, amma a dayan bangaren, ya kamata mu lura da harkokin dake gudana yadda kamata, wato a daidaita dangantaka tsakanin kasuwa da gwamnati. Gina tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci dake tsibirin Hainan, ba zai kwaikwayi yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati ba."

A yayin da annobar COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a duk fadin duniya, shirin ya kuma bayyana cewa, ya kamata a kafa tsarin rigakafi gami da shawo kan hadurra, a wani mataki na magance hadurran da ka iya kunno kai a bangarorin da suka shafi cinikayya, da zuba jari, da hada-hadar kudi, da musanyar alkaluman kididdiga, da muhallin halittu da kiwon lafiya da sauransu. Wani babban masani mai nazarin yankunan cinikayya cikin 'yanci na kasar Sin Li Guanghui ya bayyana ra'ayinsa cewa:

"Na farko, ina tsammanin akwai bukatar a shawo kan hadurran tsaro na kasa, na biyu, ya kamata a shawo kan hadurran da suka shafi tattalin arzikin kasar, ko kuma wadanda za su iya haifar da babbar barazana ga zaman rayuwar al'umma."

A nan gaba, tashar cinikayya ta ruwa cikin 'yanci dake tsibirin Hainan za ta zama wani kyakkyawan misali na bude kofar kasar Sin ga kasashen ketare, wadda za ta kara taka rawar a-zo-a-gani a fannin dunkulewar tattalin arzikin duniya waje guda da raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China