Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabuwar dokar kare namun daji ta fara aiki a birnin Beijing
2020-06-02 10:05:24        cri
Hukumar kula da muhallin halittu ta birnin Beijing, ta bayyana cewa, sabuwar dokar kare namun daji da aka fito da ita, ta fara aiki jiya Litinin a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Jami'i a hukumar Zhang Zhiming ya bayyana cewa, karkashin sabuwar dokar, birnin Beijing zai haramta yin farauta a tsawon wannan shekara da kara yanke hukunci kan duk wasu ayyukan masu nasaba da namun daji da suka saba doka.

Ya ce, wannan ita ce doka mafi tsauri a tarihin birnin na Beijing game da kare namun daji, za kuma ta samar da tabbacin doka mai karfi kan matakan birnin na kare namun daji.

Dokar ta bayyana cewa, idan har dabbobi suna karkashin kariya ta musamman ne, to za a ci tarar wadanda suka yi farautar su, tara tsakanin ninki biyar zuwa goma na darajar dabbobin da aka yi farautarsu, baya ga tarar sama da Yuan dubu biyar, kwatankwacin dala kimanin 700 da kuma tarar kasa da Yuan dubu ashirin (20,000), ko da masu farautar ba su kama komai ba.

Haka kuma, dokar ta kunshi kare namun daji dake bisa doron kasa, gami da muhallin halittu na musamman, bisa tsarin kimiya da zamantakewar al'umma da inganta matakan kare muhallin halittu. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China