Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dokar tsaron kasa da na kundin zamantakewar al'umma na kasar Sin
2020-06-04 09:34:32        cri

Yauzu dai ta tabbata cewa, zaman taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, ya kada kuri'ar amincewa da kundin dokar zamantakewar al'umma da aka dade ana tsammani.

Baya ga manyan tanade-tanade da kanana kudurori, kundin zaman takewar al'umma, shi ne kundin dokar zaman takewar al'umma irin sa na farko a sabon zamani da ake ciki a duniya, yana kuma da sassa shida da suka shafi hakkin bil-Adama, da 'yancin rayuwa, da batun da ya shafi aure da iyali da gado da biyan diya kan barnar da aka haddasa da sauran fannoni da suka shafi zamantakewar yau da kullum.

Wakilan sun bayyana cewa, gyara fasalin dokar, ba ya nufin kafa sabuwar doka game da zamantakewar al'umma, maimakon haka wani tsari na sanya dokoki da ka'idojin da ake amfani da su a baya, da yi musu gyaran fuska da kuma inganta su, ta yadda za su dace da sabbin yanayin da ake ciki a wuraren da za a aiwatar da su.

A hannu guda kuma, an amince da dokar tsaron kasa, Wannan shi ne karo na farko da aka kafa wata doka da sunan kundin doka mai kunshe da ayoyi da dama a kasar Sin, da zummar kara karfafa tsaro a duk fadin kasar, da inganta tushen manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu", ta yadda za'a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin na Hong Kong.

A ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2021, ake sa ran dokar za ta fara aiki. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China