Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Daliban kasar Sin na komawa makarantunsu
2020-06-01 13:45:12        cri

Yau 1 ga wata, ranar yara ce ta duniya. Kuma a kwanakin nan, daliban dake sassa da dama na kasar Sin suna komawa makarantunsu domin farfado da karatu.

A yau, dalibai sama da dubu 400 daga aji na 1 da na 2 na makarantun sakandare, da na midil, gami da na aji na 6 na makarantun firamare a Beijing sun koma karatu a makarantunsu. Nan gaba kadan wato ranar 8 ga wata, dalibai daga aji na 4 da na 5 na makarantun firamare a Beijing su ma za su koma karatu a makaranta. Kwamitin kula da harkokin ilimi na Beijing ya ce, buri na farko a halin yanzu shi ne maida hankali kan lafiyar daliban gami da abun da suke tunani a kai.

Tun daga tsakiyar watan Mayu, a yayin da ake kokarin dakile yaduwar annobar COVID-19, ma'aikatar ilimin kasar ta himmantu wajen farfado da karatun dukkan dalibai a makarantu daban-daban, da gaggauta maido da harkokin koyarwa na yau da kullum. Sassa daban-daban na kasar Sin ma sun tsara nasu shirye-shirye na farfado da karatu a makaranta.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China