Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a tarukan NPC da CPPCC
2020-05-28 12:45:43        cri

Da yammacin ranar Alhamis 21 ga watan Mayun shekarar 2020 ne, aka bude taron shekara-shekara, na majalissar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin, ko CPPCC a takaice. Sannan da safiyar ranar Juma'a 22 ga watan, aka bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar, ko NPC a takaice.

A duk shekara, wannan taro na CPPCC, da ma taron majalissar wakilan jama'ar kasar Sin na NPC, kan jawo hankulan al'ummun duniya kwarai da gaske, kasancewar tarukan su ne mafiya muhimmanci dake kokarin mayar da hankali kan harkokin siyasa, da salon jagoranci a kasar Sin.

Sai dai duk da sauyin lokutan gadanar da wadannan taruka, manufofin taron CPPCC da aka bude ba su sauya ba.

Shugaban kasar Xi Jinping, da sauran shugabannin kasar Sin sun halarci zaman bude taron majalissar CPPCC na 13, wanda ya gudana a babban dakin taruwar jama'a dake nan birnin Beijing.

Daga cikin batutuwan da aka tattauna sun hada da batun kyautata mu'amula tsakanin JKS da jama'a da kyautata rayuwar manona da raya yankunan karkara, da batun kawar da jama'a daga kangin talaucin, ganin cewa, wannan shekata ta 2020, ita ce shekarar karshe dangane da shirin kasar na gina al'umma mai matsakaicin wadata.

Bugu da kari, Kasar Sin ta kara jaddada cewa, ba ta da wata manufa kan wata kasa ko shiyya ko wani buri da ya shafi tattalin arziki. Haka kuma kasar Sin ba ta da wata manufar siyasa kan taimakon da take baiwa kasashen duniya game da yaki da COVID-19.

Muhimman tarukan biyu na bana, sun tabo batun samar da aikin yi, da daidaita hadarin da ake fuskanta gami da Inganta harkokin sayayya da na kasuwanni,da martaba manufar bude kofa da yin gyara-gyare, da Kiyaye ci gaban tattalin arziki

Batutuwan da suka shafi kananan kabilu, raya yankunan musamman na HK,MCm Gabobi biyu na yankin Taiwan da manufofin diflomasiyar kasar Sin da kuma karfafa alakar Sin da kasashen Afirka, sun kasance a jerin abubuwan da aka tabo a tarukan na bana. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China