Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Har yanzu wasu 'yan siyasar yammacin duniya suna mafarki kan batun Hong Kong
2020-05-26 19:49:00        cri
A yayin taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin dake gudana a halin yanzu, an sanar da saka batun tsarawa da inganta dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin musamman na Hong Kong gami da tsarin aiwatar da ita a cikin ajandar taron. Daga baya, wasu 'yan siyasar kasashen yammacin duniya, ciki har da sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, sun bayyana cewa, wai wannan matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka zai kawo karshen tsarin cin gashin kai da ake aiwatarwa a Hong Kong, kana, suna barazanar sanyawa kasar Sin takunkumi.

Kiyaye tsaron kasa, batu ne da ya shafi muhimman muradun kowace kasa a duniya. Kuma tun bayan da yankin Hong Kong ya dawo hannun kasar Sin, bisa ka'ida ta 23 cikin babbar dokar Hong Kong, gwamnatin tsakiya ta kasar ta dankawa yankin izinin kafa dokarta ta fannin kiyaye tsaron kasa. Amma kawo yanzu, ba'a kammala aikin kafa dokar ba, al'amarin da ya sa Hong Kong ya zama wani wurin dake fuskantar rashin doka a bangaren tsaron kasa.

Tun shekarar da ta gabata, akwai wasu bata-gari da masu tsattsauran ra'ayi dake adawa da gwamnati wadanda suka yi yunkurin balle Hong Kong daga kasar Sin, da cin zarafi gami da lalata tambari da tutar kasa, da zuga al'umma don su kewaye ofishin gwamnatin tsakiya dake Hong Kong, da kai hari kan mai uwa da wabi, da fatattakar 'yan sanda, al'amuran da suka kasance ayyukan ta'addanci, da haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Hong Kong gami da cikakken iko na kasa.

Yanzu majalisar wakilan jama'ar kasar Sin tana kokarin tsarawa da inganta dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin musamman na Hong Kong gami da tsarin aiwatar da ita, da zummar kara karfafa tsaro a duk kasa, da inganta tushen manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu", ta yadda za'a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a yankin na Hong Kong.

Dalilin da ya sa wasu 'yan siyasar Amurka suka maida irin wannan martani shi ne, domin damuwar da suke yi na cewa, idan gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kara inganta dokar kiyaye tsaron kasa ta yankin Hong Kong, ba za su samu damar yin shisshigi a harkokin yankin ba, sannan yunkurinsu na kawo tsaiko ga ci gaban kasar Sin ta hanyar fakewa da yankin na Hong Kong zai bi ruwa. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China