Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a zai inganta aikin gudanar da harkokin kasar
2020-05-25 20:50:17        cri

Batu mafi muhimmanci yayin manyan taruka biyu na kasar Sin wato NPC da CPPCC na bana, shi ne duba daftarin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a. Idan aka zartas da shi bayan an duba shi, to zai kasance doka ta farko da aka kafa a matsayin kundi tun bayan da aka kafa sabuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, wanda ake kiransa "kundi dangane da bayanan da suka shafi fannoni daban daban kan zaman rayuwar al'umma", da "kundin sanarwa game da kiyaye ikon harkokin jama'a".

Tun lokacin da aka kafa sabuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, aka shigar da aikin tsara kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a a cikin ajandar kasar, amma ba a cimma wannan buri ba sakamakon rashin nagartattun sharudda. Tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, ko da yaushe jam'iyyar mai mulkin kasar tana ba da muhimmanci kan aikin gudanar da harkokin kasar bisa doka. A yayin cikakken zama na 4 na kwamitin tsakiya na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar, an gabatar da wannan muhimmin aiki na tsara kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a, yanzu an kammala wannan aiki bayan shafe kusan tsawon shekaru 5.

Bayanai na nuna cewa, daftarin kundin dokar da aka gabatar wa babban taron NPC don dubawa, yana kunshe da sassa guda 7 da ayoyi 1260, inda aka yiwa wasu dokoki da tsare-tsaren da suka shafi harkokin jama'a gyaran fuska, haka kuma an yi la'akari da sabbin matsalolin da suka bulla cikin sabon halin da ake ciki tun bayan aka soma bude kofa ga kasashen ketare da yin kwaskwarima a cikin gida, inda kuma aka fi dora muhimmanci kan aikin tafiyar da harkokin al'umma a nan gaba.

A yayin manyan taruka biyu, ana duba daftarin dokar da ya shafi harkokin jama'a, saboda kasar ta Sin na cikin wani muhimmin lokaci game da cimma burin kafa al'umma mai matsakaicin wadata a dukkan fannoni a bana. Bisa ga ci gaban tattalin arziki da karuwar wadata ta jama'ar kasar, ta sa bukatun Sinawa a fannonin demokuradiyya, dokoki, adalci, zaman daidai wa daida, tsaro da muhalli da dai sauransu sun karu. A don haka, suna fatan za a iya kara kiyaye hakkinsu yadda ya kamata. Bisa wannan yanayin da ake ciki, ana iya cewa, aikin kaddamar da kundin dokar ya zo lokacin da ya dace.(Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China