Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da samar wa kasashen Afirka gudummawar yaki da cutar COVID-19
2020-05-25 20:04:25        cri
Bisa labarin da aka bayar, an ce, ayarin jami'an lafiya da kasar Sin ta tura zuwa Congo Brazzaville, sun isa kasar a ranar 23 ga wata, jami'an lafiyar sun tashi zuwa kasar ce bayan sun kammala aikinsu a kasar Congo Kinshasa. A game da wannan, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Zhao Lijian a yau Litinin ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka gwargwadon karfinta, kuma za ta tura karin ayarin jami'an lafiya zuwa Afirka, don raba fasahohinta da kasashen Afirka.

A yayin taron manema labarai da aka shirya a wannan rana, kakakin ya ce, bisa bukatar da gwamnatocin kasashen Congo Kinshasa da Congo Brazzaville suka gabatar, a kwanan nan, kasar Sin ta tura wani ayarin da ke kunshe da masana yaki da annoba 12 zuwa kasashen biyu.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China