Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bayani kan daftarin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a
2020-05-24 19:17:12        cri

 

Yanzu dai daftarin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a ya fara zaman duddubawa da babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ke yi, wannan ya nuna cewa, ba da dadewa ba za a kaddamar da wannan ainihin kundin dokar da ya shafi harkokin jama'a na Sinawa. Za ta kasance doka ta farko da aka kafa bisa matsayin kundi, da doka ta farko dake kunshe da ayoyi sama da 1000, da kuma doka ta farko dake kunshe da kalmomi sama da dubu 100 tun bayan da aka kafa sabuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Bari mu yi bayani kan wannan kundin dokar daga fannoni 5.

 

 

Da farko, an tsara wannan kundin doka ne ba sake tsarawa ba, kuma ba hada kan dokar musamman da ka'idojin da suka shafi harkokin jama'a kawai ba. Shi wani cikakken tsari ne.

Na biyu, abun da ya fi muhimmanci a cikin kundin dokar shi ne, batun harkokin jama'a, an tsara shi ne domin jama'a, wanda kuma ke dora muhimmanci kan hakkin jama'a.

Na uku, an tsara kundin dokar bisa ga yada nasarorin da aka cimma kan al'adun kasar Sin, da na dokar da ta shafi harkokin jama'a.

 

 

Na hudu, saboda muna cikin zamani na sadarwa, don haka aka kayyade kan abubuwan da suka shafi sadarwa a yayin da ake tsara kundin dokar.

Na biyar, yanzu daftarin kundin dokar na hade da ayoyi 1260, wadanda suka riga suka yi yawa, amma duk da haka ba su iya biyan bukatun da ake kan harkokin jama'a ba. Don haka, har yanzu dai ana zurfafa yin kwaskwarima kansa. (Mai fassara: Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China