Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Annobar COVID-19 abokiyar gabar Sin da Amurka ce, inji ministan wajen Sin
2020-05-24 17:07:29        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce annobar COVID-19 ta kasance abokiyar gaba ga kasashen Sin da Amurka, wacce al'ummomin kasashen biyu suke fatan goyon baya juna da taimakon juna domin shawo kanta. Wang Yi ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka shirya a yau Lahadi a nan birnin Beijing a gefen babban taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin na wannan shekara.

Sai dai abin takaici ne, yadda wasu ke yunkurin siyasantar da cutar da kokarin neman shafa wa kasar Sin bakin fenti a kasar ta Amurka, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce.

Wang Yi, ya kuma yi gargadi cewa wasu daga cikin 'yan siyasar Amurka suna yunkurin lalata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, dole ne a yi kokarin daukar matakan dakile mummunar aniyar tasu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China