Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Saifullahi Aminu Bello: Sinawa sun nuna min karamci
2020-05-19 15:33:29        cri


A cikin shirinmu na wannan mako, wakilinmu Murtala Zhang ya zanta da Saifullahi Aminu Bello, dan jihar Kano wanda ke karatun digiri na uku a fannin na'ura mai kwakwalwa dake jami'ar Xiamen a lardin Fujian dake kudancin kasar Sin. A zantawarsu, Saifullahi Bello ya ce, akwai bambanci sosai tsakanin yanayin karatu na kasar Sin da gida Najeriya, musamman yadda ake mu'amala tsakanin dalibai da malamai. Haka kuma ya ce, kasar Sin da Najeriya za su iya fadada hadin-gwiwa a fannin na'ura mai kwakwalwa, musamman a fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI a turance.

Game da kokarin da kasar Sin ta yi wajen dakile annobar cutar COVID-19, Saifullahi Aminu Bello ya ce, yanzu kura ta kusan lafawa a kasar, kuma harkokin zaman rayuwa da karatu suna komawa yadda suke a da. Ya kara da cewa, bai taba gamuwa da wata matsala da ta shafi nuna kyama ga baki 'yan kasashen waje a nan kasar Sin ba, har ma mutanen kasar Sin sun nuna masa karamci sosai. (Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China