Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta yi nasarar yaki da talauci kamar yadda aka tsara duk da COVID-19
2020-05-19 11:08:30        cri

Darektan ofishin yaki da talauci da raya kasa na majalisar gudanarwar kasar Sin Liu Yongfu, ya bayyana cewa, duk da tasirin COVID-19, kasarsa za ta iya cimma nasarar manufofin da ta sanya a gaba game da kawar da talauci a wannan shekara kamar yadda aka tsara.

Liu Yongfu ya ce, kasar Sin ta bullo da managartan manufofi don taimakawa ma'aikata 'yan ci-rani da suka makale a gida sakamamon annobar COVID-19, ta yadda za su samu ayyukan yi a wuraren da suke, a wani mataki na kare irin wadannan mutane daga sake komawa kangin talauci.

Bayanai na nuna cewa, yanzu haka kasar Sin ta kusa kammala ayyukanta na kawar da talauci, inda ya zuwa karshen shekarar 2019, yawan mutanen dake fama da wannan matsala ya ragu zuwa miliyan 5.51 daga mutane miliyan 98.99 a karshen shekarar 2012, kana yawan yankunan dake fama da talauci a wannan shekara ta 2020 da muke ciki, ya ragu zuwa 52.

Liu ya lura da cewa, kasar Sin za ta hanzarta daukar matakai wajen tsame wadannan yankuna 52 dake fama da talauci da kauyuka 1,113 daga kangin talauci, za kuma ta cimma wannan nasara ce, ta hanyar mayar da hankali kan biyan bukatun al'ummomin dake fama da talauci ta hanyar samar da tsarin Ilimi na tilas, da kiwon lafiya, da gidajen kwana masu inganci da ruwan sha mai tsafta.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China