Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar COVID-19 a Afrika ya kai 2,074, yayin da na wadanda aka tabbatar sun kamu ya kai 54,027
2020-05-09 17:03:47        cri
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka da kandagarkinsu ta Afrika wato Africa CDC, ta ce zuwa jiya Juma'a, adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar COVID-19 a nahiyar ya kai 2,074 yayin da na wadanda aka tabbatar sun kamu ya kai 54,027.

Cikin sabon rahoton da ta fitar kan yanayin cutar a jiya, cibiyar ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ya tashi daga 51,698 a ranar Alhamis, zuwa 54,027 da yammacin jiya Juma'a, wanda ya nuna an samu sabbin mutane 2,329 da suka kamu cikin sa'a 24.

Cibiyar wadda ta ce kawo yanzu cutar ta bulla a kasashen nahiyar 53, ta kuma bayyana cewa akwai mutane 18,636 da suka warke daga cutar ya zuwa jiyan, wanda ya nuna cewa an samu sabbin mutane 1,046 da suka warke akan 17,590 da ake da su a ranar Alhamis. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China