Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana ne kadai za su tabbatar da asalin kwayar cutar COVID-19
2020-05-07 15:28:21        cri

A 'yan kwanakin baya, wasu masana na kasar Australiya, wadanda suke nazarin ilmin kwayoyin cuta da na annoba sun bayyana cewa, har yanzu ba a samu shaidar dake tabbatar da zaton "kwayar cutar Korona ta bullo daga dakin gwaji" ba.

A watan Maris, wata tawagar nazari ta kasa da kasa da Farfesa Edward Holmes wanda ke nazarin ilmin kwayoyin cuta a jami'ar Sydney ta kasar Australiya ya taba aiki da ita, ta wallafa wani bayani a mujallar "Nature Medicine" ta kasar Birtaniya, inda aka nuna cewa, bisa nazarin da aka yi, shaidu sun bayyana cewa, har yanzu babu wanda ya san asalin kwayar cutar COVID-19. Farfesa Edward ya ce, bisa ilmin kimiyya, kawo yanzu ba a samu wata shaida dake tabbatar da cewa, dan Adam ne ya kirkiro kwayar cutar ba.

Mr. Nigel McMillan, direktan sashen nazarin cututtukan annoba a cibiyar nazarin kiwon lafiya ta Menzies ta jami'ar Griffith ta Queensland ya shaidawa menama labaru cewa, kawo yanzu, dukkan shaidu sun tabbatar da cewa, sabuwar kwayar Korona, cuta ce da ta bullo daga indallahi, amma babu wanda ya kirkiro ta. Mr. Mcmillan ya kara da cewa, dukkan samfuran da aka samu a fadin duniya sun bayyana cewa, dangin kwayar cutar Korona, kwayoyi ne da aka samu a jikin jemage da pangolin. Har yanzu akwai bukatar kara yin nazari kan yadda kwayoyi dake jikin wadannan dabbobin daji biyu suka hadu suka zama wata sabuwar kwayar Korona. Ya nanata cewa, irin wannan sauyi ne da aka samu ba zato daga indallahi, amma babu wanda ya kirkiro ta.

A kwanakin baya ma,mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniya WHO Fadela Chaib, ta bayyana cewa, dukkan shaidu sun yanke shawarar ce, cutar numfashi ta COVID-19 na da asali da dabba, kuma ba wani ne ya kirkiro ko ya samar da ita a dakin bincike ko a wani wuri ba.

Fadela ta ce, "WHO ta fada, kamar yadda na bayyana cewa, a matsayinta na hukuma dake kware a fannin kimiya, muna tunanin cutar ta samo asali daga dabba," watakila akwai ta a jikin jemaga, amma har yanzu ba a gano yadda dan-Adam ke daukar cutar daga jikin Jemagen ba.

Ta kara da cewa, hakika akwai dabbar dake yada wannan cuta daga Jemagu zuwa jikin dan-Adam. A don haka, ta yi alkawarin cewa, WHO tana maraba da dukkan kasashe, da su goyi bayan kokarin da ake yi na gano asalin kwayar cutar, tana mai cewa, kungiyoyi da dama, ciki har da masanan kasar Sin, suna can suna kokarin gano asalin wannan kwayar cutar.

Don haka, batun nuna yatsa ga wata kasa ko yanki game da asali kwayar cutar da ma munanan kalaman da wasun kasashen yamma ke yi wai, wata kasa ta biya diyya dangane da wannan cuta, bai ma taso ba. Yanzu lokaci ne na hada kai don ganin wannan annoba. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China