Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wasu 'yan siyasar Amurka suna da alaka da saurin yaduwar COVID 19 a duniya
2020-05-02 19:47:56        cri

Wasu 'yan siyasar Amurka maras imani da wasu kafofin watsa labaru na Amurka sun zama inuwa guda wajen dora laifi kan kasar Sin, har ma sun ihun neman kasar Sin ta biya kudin diyya kan cutar, amma idan an waiwayi matakan da gwmanatin Amurka ta dauka wajen yakar cutar, ana iya ganin cewa: matakai ne masu cike da kuskure, kuma manufofi marasa imani da wasu 'yan siyasar Amurka suka dauka na haifar da saurin yaduwar cutar a kasar, har ma a duk fadin duniya baki daya.

Na farko, cuta ba ta san kan iyakokin kasa da kasa, tana yaduwa a duk fadin duniya. Sabo da haka, ya kamata, duk kasashen duniya sun yi hadin gwiwa wajen na tinkarar cutar. Amma, Sabo da manufofin kuskure da mahukuntan Amurka ta dauka da kuma yunkurin siyasantar da batun sun haddasa yawan mutanen da suka kamu da cutar, kuma yawan matata sakamakon kamuwa da cutar dukkansu sun karu cikin sauri sosai, abin da ya kawo matsin lamba sosai ga duk duniya wajen yakar cutar.

Na biyu kuwa, mahukunta Amurka ta dinga aiwatar manufar "Amurka na gaban kome" a yayin da ta dauk matakan kandagarkin cutar domin cin moriyarsu kawai. Alal misali, sun sanar da tsananta matakin tesa keyar makaurata ta barauniyar hanya daga Mexico da kasashen nahiyar tsakiyar Amurka a dai dai wannan lokaci, abin da ya haifar da kalubale matuka na yaduwar cutar a duniya, har ya jefa duk duniya cikin mawuyacin hali.

Na uku kuma, a kwanakin baya, Amurka ta sanar da daina tallafawa WHO, har ma Mike Pompeo ya yi barzanar daina samarwa hukumar tallafi har abada, ban da wannan kuma ya yi kirari cewa, wai kasar za ta kafa wata kungiya ta daban don maye gurbin WHO. Abubuwan dake nuna cewa, Amurka ta mai da duk wata kungiyar kasa da kasa matsayin matakin kare moriyar kasar Amurka kawai, idan ba ta da amfani sai ta yi watsi da ita.

COVID-19 da har yanzu ba a shawo kan ta ba, matsala ce da ta fi kawo barazana ga duk fadin duniya tun bayan yakin duniya na biyu. Ba za a iya shawo kan ta ba, sai dai kasa da kasa sun hada kansu. Idan 'yan siyasar Amurka suka yi biris da wannan, har suka ci gaba da bin hanya da ba ta dace ba, tabbas ne jama'ar duk duniya za su zarginsu da aikata laifi, su kuma za su zama masu aikata babban laifi ga tarihin bil Adam. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China