Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shi Donald Trump ya san tsananin kalubalolin da duk duniya ke fuskanta yanzu kuwa?
2020-05-03 18:23:29        cri

Babu tabbas game da ko shugaban kasar Amurka Donald Trump ya san tsananin cutar COVID-19 ko a'a. Bayan watanni uku da wani abu da bullowar wannan mumunar cutar, har zuwa yanzu dai, yawan mutanen da suka kamu da cutar a Amurka ya haura miliyan 1, kimanin Amurkawa dubu 60 sun rasa rayukansu a kasar, ga kuma yadda tattalin arzikin kasar ke fuskantar yiwuwar koma baya.

Trump ya taba bayyana cewa, shi ya fi sojoji kwarewa ta fuskar fahimci ISIS, kuma hazaka da yake nunawa a fannin kimiyya, ta baiwa masu kimiyya mamaki sosai, har ma yana alfahari kan matakan da yake dauka a dukkan fannoni.

Amma a cikin wannan rikici wanda ya fi tsanani bayan yakin duniya na biyu, halayen jagorancin Donald Trump na cike da kuskure, da karancin bayanai, da yanke shawara mai hadari, da kuma alakanta harkar da siyasa matuka.

Yayin da ya zanta da dan jaridar CNN Jim Acosta kwanan baya, Donald Trump ya zargin wasu masana da kuma fitattun mutane da cewa, suna ganin cewa, wannan cuta ba za ta kawo illa ga Amurka ba, dukkansu sun yi kuskure, ba su yi hasashe kan tsanantar da cuta ta yi ba. Irin wannan hujja sau da dama Trump ya kan gabatar da ita, don dora laifinsa ga sauran mutane.

Babbar daraktan cibiyar CDC ta Amurka Nancy Messonnier, ta taba yin gargadi a ran 27 ga watan Fabrairu cewa, ko shakka babu wannan cutar za ta yi saurin yaduwa a Amurka, kuma halin da ake ciki zai kara tsananta, amma Trump ya dauki wasu matakai na siyasa, don gudun sauke nauyin dake wuyansa, kamar su murguda gaskiya, da baza jita-jita. Duk matakan da yake dauka na nufin kyautata mutuncinsa, don samun zarcewa a yayin zabe, kuma irin wannan mataki ya taimaka masa wajen janye jikinsa daga rikicin tsigewa da aka yi masa a baya.

Ban da wannan kuma, Trump ya kan fadi abubuwa dake sabawa da shawarwarin wasu masana a fannin kiwon lafiya. Alal misali, ya taba gayawa manema labarai cewa, za a iya sha, ko yin allurar ruwan kashe kwayar cuta don kandagarkin COVID 19. Wasu Amurkawa sun gwada wannan mataki, kuma babu shakka hakan zai lalata lafiyar jikinsu. Har ma an ba da labarin cewa, Trump ya kalubalanci makarantu da su sake bude kofa, to amma idan yara sun taru, dimbinsu sun kamu da cutar, ko Trump zai kashe kudi don yi musu jiyya? Wa zai tabbatar da lafiyar yaran?

 

Haka zalika, CNN ta ba da labarin cewa, kamfani mafi girma a Amurka mai sarrafa naman dabbobi na Tyson Waterloo, ya yanke shawarar rufe sassansa har kashi 80% a kasar, don hana ma'aikatansa kamuwa da wannan cutar. Amma nan da nan, Trump ya umurce su, da su ci gaba da aiki a masana'antar bisa dokar samar da kayayyaki masu alaka da tsaron kasar. Shi dai ba ya mai da hankali kan ma'aikata Amurkawa ko kadan?

Dadin dadawa, Trump ya ba da sako a kan shafin sa na Twitter a kwanan baya, yana mai cewa, jihohi da dama za su sake bude kofofinsu cikin sauri da lafiya, amma zuwa yanzu adadin wadanda suka kamuwa da cutar a Amurka sun haura miliyan 1. Shin ko ba ya la'akari da lafiyar jama'ar Amurka ne ko kadan?

Duk da wadannan matakai masu ban dariya da Donald Trump ya dauka, kafofin yada labarai na Amurka, wadanda suke goya masa baya ba tare da wani dalili ba, suna iyakacin kokari kare shi, suna kai hari kan daidaikun mutane, ko kungiyoyi, ko kasashe da suke nuna shakku game da shi, musamman ma zargin kasar Sin, domin dora laifinsa kan kasar Sin da boye laifin da ya aikata. (Marubuta: Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China