Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda mata suke a matsayinsu na mata, uwa, 'ya da kuma 'yar uwa
2020-05-05 14:44:10        cri

Bullar cutar numfashi ta COVID-19 a farkon wannan shekara, wadda yanzu haka ta watsu zuwa wasu sassa na duniya, ta kawo illa ga daukacin bil Adam. Wannan annobar ta yi tasiri da kuma canja yadda zaman rayuwarmu yake, bisa wannan yanayin da muke ciki, 'yan uwanmu mata sun fi taka rawa bisa na da a zaman rayuwar yau da kullum, musamman ma a cikin gidajensu.

Malama Liang, ba ta fita aiki sai zaman kula da iyali. Mijinta likita ne a wani shahararren asibiti, ta gaya mana cewa, bayan bullar cutar numfashin, yawancin Sinawa na zaune ne a gida kamar yadda gwamnati ta ba da shawara, amma a matsayinsa na likita, mijinta yana ci gaba da aiki kamar kullum, don haka ta damu sosai da lafiyar mijinta. Ta ce, dole ne ta yi kokarin karfafawa mijinta gwiwa kan aikin da yake na yaki da wannan cuta.

"A matsayi na na matar likita, abun da nake iya yi a yanzu shi ne, kara mayar da hankali kan dafawa mijina abinci mai kyau da zai samu isassun sinadarai masu gina jiki, ta yadda zai samu karfi da lafiya wajen gudanar da aikinsa. Ya kamata in yi kokarin tabbatar da lafiyarsa."

Masu sauraro, a cikin shirinmu na baya, mun taba gabatar muku cewa, sakamakon yanayin annobar, dukkan makarantun dake fadin kasar Sin sun yanke shawarar jinkirta lokacin fara zangon karatu. Batun ba da ilmi, muhimmin aiki ne dake jawo hankulan dubun-dubatan iyalai a nan kasar Sin. Domin kawar da tasirin da annobar ka iya yiwa dalibai kan harkokinsu na karatu, hukumomin ba da ilmi na kasar Sin suka bullo da matakin koyarwa ta yanar gizo a yawancin yankunan kasar, saboda wannan wani sabon tsari ne da aka gwada a fannin ba da ilmi, akwai bukatar malamai su kara kokarin da ba a taba ganin irinsa ba kan wannan aiki.

Malama Hu, ta taba aiki a wata jarida na shekaru biyu, bayan ta haihu sai ta bar aikin, ta dawo kulawa da 'yarta a gida. Yanzu 'yarta tana aji na biyu a makarantar firamare. Yanzu, kusan watanni uku da suka wuce da aka bullar cutar COVID-19 a kasar Sin, ta ce, ko da yake yanayin annobar ya yi kawo matsi, ita da 'yarta sun yi amfani da wannan lokaci wajen yin wasu abubuwan da ba su iya yi ba a baya. Malama Hu ta ce,

"Ga misali, maimaita abubuwan da ta koya sau da dama wajen buga kayan kida na Accordion, yanzu tsawon lokacin da 'ya ta take dauka wajen yin bita ya kai yadda nake fata. Ban da wannan kuma, na bukaci ta rika rubuta harkokinta na yau da kullum a ko wace rana, mu kan tattauna abubuwan da za a rubuta tukuna, daga baya kuma sai ta fara rubuto. Ana iya cewa, mun cimma burinmu a wasu fannoni."

                        

    Zane-zanen da 'yar malama Hu ta yi game da buga kayan kida

 

Malama Hu ta kara da cewa, saboda 'yarta tana gida a kullum, aikin na yawa fiye da a baya, ban da bitar karatu da 'yarta, ta na kuma kulawa da sauran abubuwan rayuwarta, ciki har da dafa mata abinci.

"Na kan yi ayyuka daban daban masu yawa daga sassafe har zuwa dare, don haka, kwanan nan na kan yi saurin fushi, da kyar nake iya sarrafa hankali na. Amma, idan an komo makaranta, to za mu tsara shirinmu bisa bukatar makarantar, idan na tunana haka, hankali na ma ya kan tashi."

Malama Jiang, 'yar kasuwa ce dake sayar da kayayyaki ta yanar gizo, tun bayan bullar cutar, sai ta koma zaman gida, tana taya 'danta dake aji 4 a makarantar firamare karatu, ta kuma bayyana ra'ayinta game da ba da darasi a yanar gizo,

"Irin tsarin karatun na da kyau, saboda idan yara ba su fahimci abun da malamai suka koya musu sosai ba, to su na iya maimaita kallon bidiyo sau da yawa har su fahimta, wannan abu ne da ba a iya yi a makaranta. Amma, abu marasa kyau shi ne, kallon bidiyo ta kamputa na tsawon lokaci, zai illata idannun yara, ban da wannan kuma, ba su iya mu'amala da malamai fuska da fuska."

Malama Jiang da 'danta

 

Malama Jiang ta ce, 'danta ya kan samu wasannin intanet daga shafin yanar gizo a cikin gida, amma ba zai yiwu ba ya samu damar yin haka a makaranta, don haka, akwai bukatar iyaye su kula da su sosai. A karshe dai, ta bayyana fatanta kan 'danta,

"Ina fata zai kasance mai koshin lafiya, kuma ina fata bisa kokarin da yake yi, zai iya bada gudunmuwa a cikin al'umma."

Masu sauraro, kafinmu watsa wannan shirin na yau, daliban dake karatu a makarantun sakandare wadanda ke fuskantar jarrabawar kammala karatu a nan birnin Beijing, sun riga sun koma makaranta, ban da wannan kuma kwanan baya birnin Beijing ya daidaita matsayin tinkarar yakar annobar, wato an rage matsayin zuwa 2, irin matakin da aka dauka a birnin Beijing da ya kasance mafi hadarin fama da annobar ya nuna cewa, yanayin annobar da duk kasar ke ciki ya sassauta. Muna fata, za a kawar da annobar a duk fadin duniya.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China