Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Namibia za ta fitar da dalar Amurka miliyan 36 domin tallafawa ma'aikata
2020-04-28 12:03:17        cri
Kasar Namibia ta sanar da ware dalar kasar miliyan 650, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 36, a matsayin tallafi ga kamfanonin yawon shakatawa da na gine-gine da na sufurin jiragen sama, domin su biya albashin ma'aikata a lokacin da dokar kulle ke gudana.

Ministan kudi na kasar Ipumbu Shiimi, ya ce gwamnati za ta bayar da dalar kasar miliyan 400, yayin da hukumar kula da jin dadin jama'a za ta bayar da dalar 250, domin taimakawa ma'aikata rike ayyukansu.

Ministan ya ce gwamnati na amfani da tallafin domin tabbatar da kasar ta ceci yiwuwar rashin aikin yi a nan gaba.

Ya kara da cewa, tallafin wani bangare ne na shirye-shiryen da aka gabatar domin ceton tattalin arzikin kasar daga durkushewa saboda kullen.

Jami'ar zartarwa ta hukumar kula da jin dadin jama'a ta kasar Milka Mugunda, ta ce hukumar ta bada tallafin ne domin tabbatar da kula da yanayin zamantakewar matalauta da masu rauni. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China