Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanan Australiya: Babu shaidar dake tabbatar da zaton "kwayar cutar Korona ta bullo daga dakin gwaji"
2020-04-21 12:57:52        cri

A 'yan kwanakin baya, wasu masana na kasar Australiya, wadanda suke nazarin ilmin kwayoyin cuta da na annoba sun bayyana cewa, har yanzu ba a samu shaidar dake tabbatar da zaton "kwayar cutar Korona ta bullo daga dakin gwaji" ba.

A watan Maris, wata tawagar nazari ta kasa da kasa da Farfesa Edward Holmes wanda ke nazarin ilmin kwayoyin cuta a jami'ar Sydney ta kasar Australiya ya taba aiki da ita, ta wallafa wani bayani a mujallar "Nature Medicine" ta kasar Birtaniya, inda aka nuna cewa, bisa nazarin da aka yi, shaidu sun bayyana cewa, kwayar cutar Korona, cuta ce da ta bullo daga indallahi. Farfesa Edward ya ce, bisa ilmin kimiyya, kawo yanzu ba a samu wata shaida da tabbatar da cewa, dan Adam ne ya kirkiro kwayar cutar ba. Mr. Edward Holmes ya bayyana cewa, "Idan wani yana son kirkiro wata kwayar Korona, a kullum, yana bukatar aikin zabe daga wasu kwayoyin Korona da yake da su a dakin gwaji. Sannan ya daidaita sashen kwayar Korona da ya zaba domin renonsu. Amma cutar COVID-19 har yanzu ba ta bayyana halayyar da dukkan kwayoyin cutar Korona da ake da su a dakin gwaji suke da ita ba. Sakamakon haka, muna da tabbacin cewa, zaton bullowar sabuwar kwayar Korona daga dakin gwaji ba haka ba ne."

Mr. Nigel McMillan, direktan sashen nazarin cututtukan annoba a cibiyar nazarin kiwon lafiya ta Menzies ta jami'ar Griffith ta Queensland ya shaidawa menama labaru cewa, kawo yanzu, dukkan shaidu sun tabbatar da cewa, sabuwar kwayar Korona, cuta ce da ta bullo daga indallahi, amma babu wanda ya kirkiro ta. Mr. Mcmillan ya kara da cewa, dukkan samfuran da aka samu a fadin duniya sun bayyana cewa, dangin kwayar sabuwar Korona, kwayoyi ne da aka samu a jikin jemage da pangolin. Har yanzu ana bukatar kara yin nazari kan yadda kwayoyi dake jikin wadannan dabbobin daji biyu suka hada suka zama wata sabuwar kwayar Korona. Ya nanata cewa, irin wannan sauyi ne da aka samu ba zato daga indallahi, amma babu wanda ya kirkiro ta.

"Da farko dai, wata hallayar da ake gani sosai ita ce, kwayar hallitar gene ta sauya ba zato ba tsammani, wato wasu sun sauya a kan jikin protein, amma wasu ba haka suke yi ba. Amma idan dan Adam ne ya kirkiro sabuwar kwayar cuta, za a canja kwayar hallitar gene dake kan jikin protein kawai. Wannan halayya ta bayyana cewa, kwayar sabuwar Korona ta bullo ne daga indallahi, babu wanda yake da fasahar kirkiro ta."

A ganin farfesa Mcmillan, babu mamaki ne bullowar matsalar sabuwar kwayar Korona. A matsayin kwararren dake nazarin kwayoyin cututtuka, ya bayyana cewa, a kullum, a shirye masu nazarin kimiyya da fasaha suke wajen fuskantar bullowar wata sabuwar kwayar cuta da ba su sani ba a da. Gwamnatocin kasashen duniya ma suna da shirin kandagarkin irin wannan sabuwar kwayar cuta. Mr. Mcmillan yana mai cewa, "Bayan an nazarci kwayar cutar Korona ta SARS da ta MERS, mun fahimci wasu ilmin kwayoyin cutar Korona. A da, kwayoyin cutar Korona sun samu sauye-sauye, a nan gaba ma za su ci gaba da samun sauye-sauye. A idon kwararru wadanda suke nazarin kwayoyin cuta, babu mamakin irin wannan sauye-sauyen da aka samu ba zato ba tsammani. A wajen gwamnati ma wannan ba abin mamaki ba ne. Kusan gwamnatin kowace kasa tana da shirin kandagarkin irin wannan annoba, amma wasu gwamnatoci, kamar gwamnatin Amurka da ta Birtaniya ba su dauki matakai kamar yadda ya kamata bisa shiri ba."

Mr. Hassan Vally wanda ke nazarin ilmin annoba a jami'ar La Trobe ta kasar Australiya ya bayyana cewa, babu shaida ko kadan dake iya tabbatar da cewa sabuwar kwayar Korona ta bullo daga dakin gwaji. Vally ya kara da cewa, "Dole ne a kula, domin kada a samar wa masu yada jita-jita wata dama." Ya kuma nuna cewa, wasu mutane suna yada jita-jita ne a yunkurinsu na cimma wani buri nasu na siyasa. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China