Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Masar ya yaba wa taimakon da kasar Sin ta ba kasashen Afirka wajen dakile COVID-19
2020-04-20 13:13:43        cri

Yanzu a lokacin da annobar COVID-19 take yaduwa a kasashen Afirka, kasar Sin ba ta bata lokaci ba wajen taimakawa kasashen nahiyar ba. Sabo da haka, malam Hussain Ismail, wanda ya kware kan nazarin kasar Sin a cibiyar nazarin harkokin siyasa ta babbar hukumar kula da aikin jarida ta kasar Masar yana ganin cewa, an samu sabbin abubuwa dangane da hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Afirka da Sin a lokacin da ake namijin kokarin tinkarar annobar.

Bayan barkewar annobar COVID-19 a fadin duniya, ba tare da bata lokaci ba, kasar Sin ta kaddamar da aikin samar da taimakon agaji ga sauran kasashen duniya. Kawo yanzu, ta riga ta tura tawagogyin kwararrun ma'akatan jinya zuwa kasashe fiye da 10, a lokacin guda kuma, tana samar da kayayyakin shawo kan annobar ga kasashe fiye da dari. Alal misali, kawo yanzu kasashen Afirka fiye da 50 sun samu kayayyakin kiwon lafiya da kasar Sin ta samar musu. Mr. Hussain Isamail ya bayyana cewa, "Yanzu a lokacin da ake cikin hali mai tsanani na yakar annobar COVID-19, kasar Sin ta samar da kayayyakin jin kai da fasahohin tinkarar annobar da ta samu ga kasashen Afirka. Sabo da haka, kasashen Afirka da dama sun fitar da wata hadaddiyar sanarwa, inda suka yaba sosai da taimakon da kasar Sin ta samar musu. Alal misali, a kwanakin baya, ministan harkokin wajen kasar Najeriya ya godewa kasar Sin saboda ta tallafawa kasarsa wajen yaki da annobar. Wasu kasashen dake arewacin Afirka, ciki har da kasar Masar su ma sun yabawa kasar Sin sabo da ta samar musu kayayyakin tinkarar annobar."

Kasar Sin ta dade tana taimakawa da kuma goyon bayan kasashen Afirka. Ta kuma yi kira ga MDD da ta "saurari karin ra'ayoyi daga kasashen Afirka." Hadin gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Afirka ma ta samu amincewa daga dimbin kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da MDD. Malam Hussain ya bayyana cewa, kasar Sin ba ta taba dakatar da manufarta ta yin hadin gwiwa bisa ka'idar sada zumunta tsakaninta da kasashen Afirka ba, kuma gwamnatin Sin da al'ummomin Sinawa, dukkansu suna bin manufar. Bugu da kari, kasar Sin tana samar wa kasashen Afirka karin taimako a lokacin da take aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare. Sakamakon haka, dimbin manyan ayyukan da take yi a kasashen Afirka suna taka rawar gani ga kokarin bunkasa masana'antu a nahiyar da kuma zamanantar da kasashenta. Duk wadannan abubuwan sun shaida yadda kasar Sin take sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na babbar kasa. Malam Hussain yana mai cewa, "A kullum a idon sauran kasashen duniya, kasar Sin, kasa ce dake kokarin sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na babbar kasa. Alal misali, a lokacin da ake samar da taimako ba tare da son kai ba, ko aka gamu da matsalolin jin kai a wasu yankunan kasa da kasa, tabbas kasar Sin kan fito ta taimaka."

Sannan Mr. Hussain yana ganin cewa, a yayin da ake tinkarar annobar COVID-19, kasar Sin ta yi kokarin samar da bayanai da kayayyaki ga kasashen da suke yakar annobar a kan lokaci, domin sauke nauyinta na babbar kasa. Mr. Hussain ya bayyana cewa, "Bayan annobar ta barke a kasar Sin, kasar Sin ta yi namijin kokarin samar da dukkan bayanan annobar filla filla ga kungiyoyin kasa da kasa da sauran kasashen duniya cikn gajeren lokaci. Sannan bayan ta kusan cimma nasarar shawo kan annobar a cikin gida, ba tare da bata lokaci ba, ta tura tawagogin kwararru masu aikin jinya zuwa kasashen Iran da Iraki da Italiya da Saudiyya da dai sauransu. Ba a taba ganin an dauki irin wadannan matakan cikin sauri kamar haka ba a duk fadin duniya."

Daga karshe dai, Mr. Hussain Ismail ya jaddada cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali na da muhimmanci ga kokarin tabbatar da bunkasar duk duniya. Dalilin da ya sa kasar Sin ta yi kokari haka shi ne, sabooda ta na taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya baki daya. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China