Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samar da guraban ayyukan yi masu yawa ta yanar gizo ga daliban dake Hubei
2020-04-16 20:35:53        cri
A karkashin jagorancin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice da kwamitin kula da kadarorin gwamnati, da kuma sashen tsare-tsare na kwamitin birnin Beijing na lardin Hubei, manhajan bidiyo da sashen ma'aikata na kamfanin raya kasa da zuba jari na kasar sun karbi bakuncin bikin daukar ma'aikata ta yanar gizo musamman na lardin Hubei. A cikin kwanaki 4, shahararrun kamfanoni sama da 500 sun samar da guraban ayyukan yi sama da 84000 masu inganci ga daliban da za su kammala karatunsu a jami'a na lardin Hubei. Daga ciki, asibitin Jin Yin Tan na Wuhan da asibitin Xie He wadanda suka kasance muhimman cibiyoyin aikin jinya na yakar cutar COVID-19 sun samar da guraban ayyukan yi sama da 1600, hakan ya kara karfin cibiyoyin lafiya na birnin Wuhan, kuma dalibai masu yawa sun gabatar da bukatunsu na neman aikin. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China