Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Najeriya da jakadan kasar Sin dake Najeriya sun yi karin haske kan batun birnin Guangzhou
2020-04-16 12:42:51        cri

A ranar Talata ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama, da jakadan Sin dake Najeriya Zhou Pingjian, sun kira taron manema labarai tare, inda suka sanar da gaskiyar abin da ke faruwa kan batun wai cin zarafin 'yan Najeriya wadanda suke birnin Guangzhou yayin da ake kokarin dakile annobar COVID-19. Mr. Geoffrey Onyeama ya ce, wani hoton bidiyon da wani dan kasuwar Najeriya ya dauka a Guangzhou ya bayyana al'amarin da ya faru a Guangzhou ba kamar yadda aka bayyana a shafukan sada zumunta ba. Gwamnatin kasar Sin na kokarin mayar da martani ga abubuwan halal da bangaren Najeriya da sauran bangarorin Afirka suke mayar da hankali sosai. Sannan an gano cewa ana kokarin warware matsalolin da suke faruwa kamar yadda ake fata. Jakada Zhou Pingjian ya kuma bayyana cewa, Birnin Guangzhou na yin namijin kokarin yaki da annobar COVID-19, ba a kan 'yan Najeriya da 'yan Afirka ko sauran 'yan kasashen waje ba.

Mr. Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ta mai da hankalinta sosai kan halin da 'yan Afirka suke, ciki har da halin da 'yan kasar suke ciki a birnin Guangzhou wadanda aka killace su da aka yada a shafukan sada zumunta. Ya kara da cewa, a kwanan baya, an samu wani shirin murya da wani dan kabilar Igbo wanda yake kasuwanci a Guangzhou ya tsara. A cikin wannan shirin murya, a bayyane ne al'amarin da ya faru a Guangzhou ya kasance ba kamar yadda wasu hotunan bidiyon da aka yada a shafukan sada zumunta na intanet suke bayyanawa ba. Ya nuna cewa, "Gaskiyar batun shi ne, an tabbatar wasu 'yan kasar Najeriya sun kamu da cutar COVID-19 lokacin da suka isa birnin Guangzhou. Daga baya kuma an tabbatar wata mace Basiniya mai shagon sayar da abinci ta kamu da cutar, wannan shagon cin abinci kuwa wuri ne da 'yan Afrika ciki har da 'yan Najeriya suke taruwa domin cin abinci. Saboda haka, gwamnatin birnin ta sanar da rufe wannan shago, tare da killace wadanda suka yi hulda da wannan matar, hakan ya sa duk mutanen da aka killace, babu shakka ba za su iya komawa otel ba, ko wuraren kwana da suka taba zama ba. Wasu 'yan Najeriya dake cikin kasar sun kalli bidiyon da ya shafi lamarin da aka yada shi a shafin sada zumunta na Intanet, sa'an nan sun yi gurguwar fahimtar cewa, wai ana nuna bambanci ga 'yan Najeriya, da ma sauran 'yan Afrika a birnin Guangzhou, yayin da ake tsaka da yaki da cutar, har kuma suka nuna rashin amincewa da hakan. Mun tuntubi ofishin jakadancinmu dake kasar Sin, da karamin ofishin jakadancinmu dake birnin Guangzhou da mukaddashin karamin jakadanmu a Guanghou, sun tabbatar da cewa, abubuwan da ake cikin wannan murya gaskiya ne."

Bugu da kari, Onyeama ya gayawa manema labaru cewa, maganar wai "ba a iya kwace takardar passport ba" ba ta yi daidai ba, mai yiyuwa ne an gamu da matsala a lokacin da ake tuntubar juna. Yanzu gwamnatin kasar Sin na kokarin mayar da martani ga abubuwan halal da bangarorin Afirka suke maida hankulansu sosai. Kuma an riga an kyautata wasu ayyuka kamar yadda ake fata. Mr. Geoffrey Onyeama yana mai cewa, "Yanzu, shafukan sada zumunta na intanet na yiwa duniyarmu tasiri sosai. A kullum wasu mutane suna bayyana ra'ayoyinsu domin yunkurin cimma burinsu. Sabo da haka, daga farko dai, na yanke shawara cewa, dole ne na dauki matakai daban daban domin warware matsalar. Wato a lokacin da nake tuntubar jakadan kasar Sin dake kasarmu, na kuma tuntubi jakadanmu dake kasar Sin da kananan jakadunmu dake biranen Guangzhou da Shanghai na kasar Sin, sannan na yi kokarin sauraron ra'ayoyin bangarori daban daban, ta yadda za a iya tabbatar da ganin mun daidaita al'amarin kamar yadda ya kamata."

A nasa bangare, jakada Zhou Pingjian ya ce, a cikin 'yan kwanakin baya, ya kan tuntubi minista Oyneama kan matakan yakar annobar da ake dauka a lardin Guangdong na kasar Sin da batutuwan da suke shafar 'yan Najeriya wadanda suke zaune a kasar Sin, sun kuma cimma matsaya daya. Jakada Zhou ya bayyana cewa, "Birnin Guangzhou na yin namijin kokarin yaki da annobar, ba ya ci zarafin 'yan Najeriya da 'yan Afirka ko sauran 'yan kasashen waje ba. A cikin 'yan kwanakin baya, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yi mu'amala da hukumomin gwamnatin birnin Guangzhou da abin ya shafa, sannan gwamnatin birnin Guangzhou ma ta yi mu'amala da karamin ofishin jakadancin kasar Najeriya dake birnin domin tabbatar musayar ra'ayoyinsu yadda ya kamata a kan lokaci. Muna kulawa da dukkan 'yan kasashen waje dake kasar Sin bisa ma'auni daya, ba mu taba daukar matakai daban daban ga wasu mutane kawai ba, har ma ba mu amince da mataki ko maganar nuna bambanci ba ko kadan."

Jakada Zhou ya kara da cewa, bisa kokarin da bangarori daban daban suke bayarwa, batutuwan dake jawo hankulan abokan Najeriya da sauran kasashen Afirka na samun warwarewa kamar yadda ya kamata. Mu Sinawa ba zamu manta da tallafi da goyon bayan da gwamnati da al'ummomin Najeriya suka samarwa kasar Sin ba a lokacin da take cikin matsanancin hali. Kasar Sin ba ta canja manufar sada zumunta tsakaninta da kasashen Afirka ko kadan ba, zumuncin dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ma ba za a iya yanke shi ba. Bangaren Sin na mutunta huldar abokantaka da aka kulla tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, Sin da Najeriya aminan juna ne, abokan arziki, kuma kyawawan 'yan uwa ne har abada. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China