Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in diflomasiyyar Sin ya bukaci a kiyaye hulda tsakanin Sin da Amurka yayin yaki da COVID-19
2020-04-16 09:57:28        cri

Yang Jiechi, mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya tattauna ta wayar tarho da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo a ranar Laraba bisa bukatar da Pompeo ya nema, inda ya bayyana cewa, ya kamata a kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka a yayin da ake tsaka da yaki da annobar COVID-19.

Yang, wanda kuma shi ne daraktan ofishin hukumar dake kula da harkokin kasashen waje na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya ce tun lokacin da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Amurka, Donald Trump, suka tattauna ta wayar tarho a ranar 27 ga watan Maris, bangarorin biyu suke ci gaba da tuntubar juna game da matakan yaki da annobar COVID-19, bisa matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma.

Yang ya bukaci bangarorin biyu su aiwatar da muhimman yarjejeniyoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma, su mayar da hankali kan hadin gwiwar dake tsakaninsu, su guji yiwa juna shisshigi, kana su mayar da hankali wajen inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ya kara da cewa, hakan shi ne muhimmin ginshikin tabbatar da moriyar jama'ar kasashen biyu da kuma biyan muradun samar da kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.

A nasa bangaren, Pompeo ya ce, annobar COVID-19 barazana ce ga dukkan al'ummar kasa da kasa, Amurka a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin don aiwatar da yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu wajen yaki da annobar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China