Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shawarar Sin kan yaki da COVID-19 ta samu goyon bayan shugabannin kasashen ASEAN da Japan da Koriya ta kudu
2020-04-15 11:27:22        cri

Jiya Talata an gudanar da taron musamman na shugabannin kasashe sha uku wato kasashe mambobin kungiyar ASEAN goma da kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu ta kafar bidiyo, ban da shugabannin kasashen 13, babban daraktan hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus da babban sakataren kungiyar ASEAN Lim Jock Hoi su ma sun halarci taron. Yayin taron, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da shawarwari kan yadda za a dakile cutar numfashi ta COVID-19, da yadda za a farfado da tattalin arziki, wadanda suka samu goyon baya daga shugabannin mahalartan taron.

Yayin taron, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya gabatar da shawarwari kan yadda za a kara karfafa aikin dakile cutar numfashi ta COVID-19, da yadda za a farfado da tattalin arziki wanda ke fuskantar matsalolin da annobar COVID-19 ta haifar.

Shugaban hukumar kula da harkokin kasashen Asiya ta ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wu Jianghao ya bayyana cewa, shawarwarin da firayin ministan kasar Sin ya gabatar sun samu goyon baya matuka daga shugabnani mahalartar taron, kana gaba daya sun dauka cewa, ya dace kasashen sha uku wato kasashe mambobin kungiyar ASEAN da kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin cimma nasarar kandagarkin annobar, a sa'i daya kuma, su yi kokari tare domin tabbatar da gudanarwar jerin ayyukan masana'antu da jerin ayyukan samar da kayayyaki, tare kuma da farfado da ci gaban tattalin arziki yadda ya kamata.

Jiya da yamma, bayan da aka kammala taron, jami'in ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wu Jianghao ya yi bayani kan abubuwan da ke da nasabar taron ga manema labarai, inda ya bayyana cewa, taron musamman da aka kira muhimmin taro ne da aka shirya tsakanin kasashen gabashin Asiya tun bayan da aka kira taron shugabannin G20, shi ma matakin yakini ne da aka dauka bisa shawarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar game da kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin ganin bayan annobar, Wu yana mai cewa, "Firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron, kuma ya gabatar da muhimmin jawabi, inda ya yi bayani kan fasahohin da kasarsa ta samu wajen kandagarkin annobar COVID-19 da raya tattalin arziki, haka kuma ya gabatar da shawarwarin kasar Sin kan yadda za a kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin dakile annobar da yadda za a daga matsayin kiwon lafiyar jama'a, tare kuma da farfado da ci gaban tattalin arziki a fadin duniya, wadannan shawarwarin sun samu goyon baya daga shugabannin mahalartan taron, gaba daya suna ganin cewa, an shirya taron ne a muhimmin lokacin da kasashen duniya suke kokarin dakile annobar, ya dace kasashen gabashin Asiya su hada kai domin ganin bayan annobar tun da wurwuri, tare kuma da raya tattalin arziki yadda ya kamata."

Wu ya kara da cewa, shugabannin kasashen da suka halarci taron sun cimma matsaya kan yadda za a hana yaduwar annobar da daga matsayin kiwon lafiyar jama'a, haka kuma sun amince da cewa, za su hada kai da hukumar lafiya ta duniya da sauran kungiyoyin kasa da kasa domin kiyaye tsaron lafiyar jama'a a fadin duniya, a cewarsa: "Shugabannin kasashen mahalartan taron sun yarda za su ci gaba da samar da bayanai da fasahohi ga juna, kana za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu wajen nazarin magungunan shawo kan cutar da allurar rigakafin cutar, ta yadda za a tabbatar da samar da isassun magunguna da kayayyakin kadagarkin cutar, ban da haka, sassan daban daban sun amince cewa, za su tattauna kan batun kafa tsarin adana muhimman kayayyakin aikin lafiya da ake bukata cikin gaggawa, domin yaki da annobar da za ta barke ba zato ba tsammani."

Wu Jianghao ya ci gaba da cewa, taron da aka kira ya kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin wadannan kasashen sha uku, shi ma ya kara karfafa gwiwar kasashen yayin da suke kokarin dakile annobar COVID-19, kasar Sin ta gamsu da sakamakon taron matuka, tana fatan za ta dauki matakai tare da kasashen domin ganin bayan annobar, tare da farfado da tattalin arziki, yana mai cewa, "Annobar tana shafar daukacin kasashen duniya, babu wata kasa da za ta tsira daga masifar, kasashen mambobin kungiyar ASEAN da kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu suna da al'adar taimakon juna a tarihi, haka kuma suna da fasahohin tattalin arziki wajen tunkarar rikicin kudi da cutuka masu saurin yaduwa misali Sars da H1N1 da Ebola da dai sauransu, a don haka ana sa ran za a cimma burin ganin bayan annobar nan da nan."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China