Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in ma'aikatar harkokin wajen Sin ya gana da jakadun kasashen Afirka da ke Sin
2020-04-14 14:52:45        cri

Jiya Litinin 13 ga watan nan, mai ba da taimako ga ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong, ya gana da wasu jakadun kasashen Afirka da ke kasar Sin, domin tattauna batutuwa masu nasaba da kandagarki, da dakile cutar COVID-19 a lardin Guangdong, da ma yanayin da 'yan Afirke ke ciki a lardin. Ganawar da ta samu halartar jakadu, da ma wakilansu daga kasashen Afirka fiye da 20.

A yayin ganawar tsakanin mai ba da taimako ga ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong, da jakadun kasashen Afirka da ke kasar Sin a jiya Litinin, Chen ya bayyana cewa, ko da yaushe, Sin na daukar al'ummar Afirka a matsayin aminanta. Kuma tun bayan barkewar cutar COVID-19, Sin da Afirka sun sake rike da hanayen juna sosai, don haye wadannan wahalhalu.

Ya ce yanzu haka cutar na yaduwa a Afirka, ko da yake Sin na ci gaba da yaki da cutar, har ma ta gaggauta samarwa kasashen Afirka kayayyakin kandagarkin cutar, baya ga yadda wurare daban daban, da ma kamfanonin Sin ke taimaka wa nahiyar ta Afirka ta hanyoyi daban daban, kamar yadda Hausawa kan cewa, bikin magaji ba ya hana na magajiya. Haka kuma a wannan lokaci na musamman, Sin da Afirka, na bukatar inganta hadin kansu, da ma kiyaye zumuncinsu. Sin za ta ci gaba da bai wa Afirka tallafi gwargwadon karfinta, wajen yaki da cutar COVID-19, har zuwa lokacin ganin bayan cutar kwata-kwata.

Ban da wannan kuma, Mr. Chen ya ce, sakamakon yaduwar cutar a duk fadin duniya, yanzu Sin na tinkarar babban kalubalen yaduwar cutar daga ketare. Ya ce lardin Guangdong na kan gaba wajen fuskantar wannan hadari, ganin yadda yake bude kofarsa ga waje sosai. Ba za a iya kiyaye sakamakon samun nasara a kan cutar COVID-19 da Sin ta sha wahala ta samu yanzu ba, har sai an kokarta kawar da duk yiyuwar sake bullowar cutar. Ya ce ana daukar matakan ne ba domin kiyaye muradun Sinawa kadai ba, har ma da sauke nauyin da ke wuyan dukkan mutanen kasashen waje ciki har da 'yan Afirka.

Haka zakila ma, game da batun da ya shafi zaman 'yan Afirka a birnin Guangzhou sakamakon daukar matakan dakile yaduwar cutar, Chen ya furta cewa, Sin na dora matukar muhimmanci a kansa. Ya ce yanzu haka gwamnatin Guangdong na kyautata matakan da take dauka, domin gudanar da ayyukan kiwon lafiya bisa ka'idar rashin nuna bambanci, sa'an nan za ta kawar da aikin killace 'yan Afirka mazauna wurin sannu da hankali, bayan tabbatar da lafiyar jikinsu, sai dai ban da masu dauke da cutar, da wadanda suka yi cudanya da su.

Bayan hakan kuma, gwamnatin na kafa tsari mai inganci, na tuntubar ofishin jakadancin kasashen Afirka dake Guangzhou. Gwamnatin kasar Sin na nuna daidaito ga dukkan mutanen kasashen waje da ke zaune a Sin, wannan kuma ita ce manufar da take bi a ko da yaushe. Don haka babu shakka za a nuna wa 'yan uwanmu na Afirka adalci, da aminci a kasar Sin.

A nasu bangaren kuma, mukaddashin jakadun Afirka da ke Sin, da ma jakadun kasashen Afirka da ke kasar, sun nuna godiya ga yadda ma'aikatar harkokin wajen Sin ta shirya wannan ganawar, a ganinsu batun ya shaida muhimmanci, da sahihanci da Sin ke nunawa Afirka, da ma aniyar warware matsala cikin ruwan sanyi.

Jakadun sun bayyana cewa, akwai dankon zumunci a tsakanin Afirka da Sin, wadanda ya sa su haye wahalhalu da yawa tare. Kuma bayan bullowar cutar COVID-19, shugabanni da jama'ar kasashen Afirka sun mika sakwanni ba tare da bata lokaci ba don goyon bayan kasar Sin. Kaza lika Afirka na godiya sosai ga yadda kasar Sin ta kula da dalibansu da ke birnin Wuhan, domin tabbatar da zamansu yadda ya kamata, da kuma lafiyar jikunansu.

Bugu da kari, jakadun sun ce, suna jinjinawa kasar Sin, bisa yadda ta samar wa Afirka goyon baya, da taimako wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19, ko da yake ita ma tana fama da cutar har yanzu. Afirka na kuma amincewa da yadda Sin ta bayar da bayani kan yanayin da Guangdong ke ciki, da ma matakan da zai dauka. Za su kuma sanar da gwamnatocin kasashensu, bayanan ba tare da boya komai ba. A sa'i daya kuma, za su sanar da 'yan kasashensu mazauna wurin, ta yadda za su aiwatar da matakan yadda ya kamata.

Sun kuma ce, Afirka na son hada kai tare da Sin, wajen sanya ido, da ma ba da jagoranci ga 'yan kasashensu da ke kasar Sin, domin su bi dokokin kasar yadda ya kamata, ta yadda za a iya dakile yaduwar cutar.

A karshe dai, jakadun Afirka da ke Sin sun yi tsokaci da cewa, Afirka da Sin aminai ne, kuma batun da ya auku a Guangdong, batu ne tsakanin 'yan uwa, kuma za a iya warware shi ta hanyar shawarwari cikin ruwan sanyi. Har ila yau ko wace kasar waje, komai yunkurin da take yi, kuma komai matakan da ta dauka, ba za ta hana ci gaban dangantakar aminci dake tsakanin Afirka da Sin ba. (Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China