Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lardin Guangdong na kokarin magance shigar da cutar COVID-19 daga ketare
2020-04-13 11:48:45        cri

Kawo yanzu, kasar Sin ta kusan cimma nasarar shawo kan cutar COVID-19 a cikin gida, amma a kullum karin masu dauke da cutar na shigowa kasar daga ketare.

Lardin Guangdong, lardi ne dake da yawan al'umma a nan kasar Sin, kuma ya zuwa shekaranjiya, ba ma kawai an gano mutane 183 wadanda suka dawo kasar Sin daga ketare, aka kuma tabbatar suna dauke da cutar ba, har ma an gano goman mutane wadanda suka kamu da sauran cututtukan dake da alaka da cutar COVID-19, da wasu mutane wadanda suka kamu da cutar amma ba su sani ba.

Abun tambaya a nan shi ne, yaya irin wadannan mutane masu dauke da cutar za su yi tasiri ga lardin? A jiya Lahadi, daya bayan daya, gwamnatin lardin Guangdong da ta birnin Guangzhou, sun shirya tarukan manema labaru har sau uku, inda aka sanar wa jama'a yanayin dakile cutar COVID-19 da ake ciki yanzu a lardin.

Yawan mutanen dake zaune a lardin Guangdong a kullum ya kai miliyan 115. Bayan an kusa shawo kan cutar COVID-19, an kusa bude dukkan masana'antu da kamfanonin samar da kayayyaki, kuma ma'aikatansu ma sun koma bakin aiki. A yayin taron manema labaru da aka shirya a jiya, Mr. Lin Keqing, zaunannen mataimakin gwamnan lardin Guangdong ya nuna cewa, sakamakon barkewar cutar a duk fadin duniya, batun yaya za a iya magance hadarin shigar da cutar daga ketare, ya zama aiki mafi muhimmanci ga lardin Guangdong a fannin dakile cutar. Lin Keqing ya nuna cewa, "Kawo yanzu, yawan 'yan kasashen waje da suke zaune a duk fadin lardin ya kai dubu 117, sakamakon haka, muna fuskantar matsin lamba sosai wajen magance shigar da cutar daga ketare. Bayan an shiga watan Maris, kwamitin jam'iyyar JKS na lardin, da kuma gwamnatin lardin, sun mayar da aikin magance shigar da cutar daga ketare gaban komai a cikin dukka ayyukan dakile cutar. Ba tare da bata lokaci ba, an kafa tsare-tsare iri 5, domin namijin kokarin magance shigar da cutar daga ketare, ta yadda za a iya tabbatar da lafiya da kuma kare rayukan dukkan mutane, ciki har da na kasashen waje dake zaune a lardinmu."

Birnin Guangzhou, kasaitaccen birni ne, kuma cibiyar kasuwanci da ta zirga-zirga ta kasa da kasa dake kudancin kasar Sin. Yawan mutanen da suka dawo daga kasashen dake cikin tsananin yanayin yaki da cutar yana da yawa. Yawan mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar ma yana da yawa a cikin lardin Guangdong.

Mr. Zhou Bin, mataimakin shugaban cibiyar rigakafi da yakar cututtuka ta Guangzhou ya gabatar da wani labari game da yadda aka gano wasu mutanen da suka kamu da cutar. Mr. Zhou Bin ya ce, "A cikin wasu mutanen da suka dawo nan Guangzhou bayan ran 8 ga watan Maris, mun gano wani mutum da ya kamu da cutar. Sannan a cikin jerin kwanaki 3, mun gano sauran mutane 4 'yan kasar waje da suka kamu da cutar. Ba tare da bata lokaci ba, nan da nan mun fara binciken dalilin da ya sa wadannan mutane suka kamu da cutar. Mun gano cewa, mutane 3 daga cikinsu sun taba cin abinci a wani karamin shagon abinci mai suna Emma Food. Hakan ya sa muka ci gaba da yin bincike kan wadanda suke da alaka da wannan shagon abinci na Emma Food. Mun gano cewa, ma'aikata da abokan mai shagon, da mijin mai shagon dukkansu sun kamu da cutar."

Ya zuwa karfe 12 na tsakar daren 11 ga watan Afrilu, jimillar mutanen da suka dawo daga ketare, kuma aka tabbatar sun kamu da cutar ya kai 119, akwai kuma wasu mutane 13 'yan kasashen waje, wadanda suka kamu da cutar sakamakon huldar su da masu dauke da cutar. Daga cikinsu, mutane 12 sun kamu da cutar ne sakamakon hulda da mutanen, wadanda suka dawo daga kasashen Afirka. Kana wani mutumin na daban ya kamu da cutar, sakamakon hulda da mai dauke da cutar daga kasar Turkiyya.

Shugaban tawagar manyan kwararru ta kwamitin kiwon lafiya na kasar Sin, kuma kwararre a hukumar ayyukan injiniya na kasar Sin, shehun malami Zhong Nanshan ya yi sharhi kana haka, yana mai cewa, ya zama wajibi sosai a dauki matakin zama a gida, da yin amfani da maganin gwaji kan wadanda suka shigo kasar Sin.

A kwanakin baya, an yi ta cacar baki sosai a shafin intanet, da shafukan sada zumunta, kan wadanda suka dawo birnin Guangzhou daga ketare, kuma suka kamu da cutar. Game da wannan matsala, shehun malami Zhong Nanshan yana ganin cewa, "Annobar numfashi ba ta san kan iyakar kasa da kasa, tana kuma yaduwa a duk fadin duniya. Hukumomin birnin Guangzhou sun riga sauran wuraren ganowa, da kuma daukar matakan magance cutar. Mun dauki matakai da suka dace, kamar zama a gida, da samar da aikin jinya ga wadanda suka kuma da cutar. Wannan kyakkyawan al'amari ne. Idan mun gano matsalar da wuri, za mu iya warware ta da wuri. Rigakafi ya fi magani." (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China